Zamfara: APC ta yi wa Matawalle jinjina kan soke dokar biyan tsaffin shugabanni fanshon makuden kudade

Zamfara: APC ta yi wa Matawalle jinjina kan soke dokar biyan tsaffin shugabanni fanshon makuden kudade

- Jam'iyyar APC a jihar Zamfara ta yi tsokaci kan doke dokar fansho na biyan makuden kudi ga tsafin shugabanin siyasa a jihar

- Alhaji Sani Gwamna da ya yi magana a madadin jam'iyyar ya ce matakin da gwamnan ya dauka abin yabo ne

- Shugaban na APC ya shawarci gwamnan ya yi amfani da kudaden wurin yi wa al'ummar Zamfara ayyukan cigaba

Kwanaki kadan bayan gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya soke dokar jihar na biyan tsaffin shugabanin jihar fansho na makuden miliyoyi, jam'iyyar APC a jihar ta bayyana matsayan ta a kan lamarin.

A cewar Kamfanin Dillancin Labarai na kasa (NAN), jam'iyyar ta APC a jihar Zamfara ta ce ta yi maraba da matakin da gwamnan ya dauka ta kuma yi masa jinjina.

Legit.ng ta gano cewa mataimakin shugaban jam'iyyar APC a mazabar Central, Alhaji Sani Gwamna ya ce ayi amfani da kudaden da za a samu bayan soke dokar wurin yi wa al'ummar Zamfara ayyukan cigaba.

Gwamna ya bayyana hakan ne a ranar Asabar 30 ga watan Nuwamba bayan taron da jam'iyyar ta gudanar.

Jam'iyyar ta APC ta ajiye adawa a gefe guda ta yabawa matakin da gwamnan jihar ya dauka duk da cewa yana jam'iyyar PDP ne.

DUBA WANNAN: Ra'ayin Aisha Buhari da na Sarkin Musulmi sun banbanta kan dokar soshiyal midiya

A baya, Legit.ng ta ruwaito cewa Gwamna Matawlle a ranar Laraba 27 ga watan Nuwamba ya saka hannu kan sabuwar doka da ta shafe tsohuwar dokar na bawa tsaffin shugabanin miliyoyin kudi a matsayin fansho.

A jawabinsa yayin saka hannu kan dokar, Gwamna Matawalle ya ce za ayi amfani da kudaden wurin yiwa al'ummar jihar ayyukan cigaba da samar da ayyukan yi ga matasa a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Online view pixel