Boko Haram: Soji sun ceto Likita, Unguzoma, da wasu mutane 18 a Yobe

Boko Haram: Soji sun ceto Likita, Unguzoma, da wasu mutane 18 a Yobe

Hukumar Sojin Najeriya a ranar Asabar ta ceto mutane 20 da yan kungiyar Boko Haram suka sace a harin da suka kai Babban Gida, hedkwatan karamar hukumar Tarmuwa na jihar Yobe ranar Alhamis.

Jami'in yada labaran hukumar, Kanal Aminu Iliyasu, ya bayyana hakan ne a jawabin da ya saki yana mai cewa:

"Za ku tuna cewa wasu yan Boko Haram sun kai hari Babban Gida, hedmwtaar karamar hukumar Tarmuwa ta jihar Yobe ranar 27 ga Nuwamba, 2019."

"Yan ta'addan sun silale cikin unguwa da motocin yaki tara domin tayar da tarzoma da kashe Sojojin da ke aiki a wajen."

"A harin, yan ta'addan sun sace dukiyoyin mutane kuma sun yi garkuwa da wasu domin shigar dasu Boko Haram."

"Amma jami'an sojin rundunar Operation LAFIYA DOLE tare da gudunmuwar mayakan sama sun yi artabu da yan ta'addan na tsawon sa'a daya kafin suka arce."

"Sai rundunar Sojin suka kure musu gudu inda suka ga gawar daya daga cikinsu da roka daya. Komai ya daidai a unguwar yanzu."

A bangare guda, wasu yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun kai mumunan hari jihar Adamawa inda suka hallaka jami'an yan sanda biyu tare da awon gaba da mutane bakwai.

Shugaban karamar hukumar Mubi ta kudu, Ahmadu Dahiru, ya bayyanawa manema labarai cewa maharan sun aikata ta'asan ne a hanyan Mubi zuwa Gyela ranar Talata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel