Nanfe Joy Jatau: Budurwa mai digiri da ta cire girman kai take wankin mota

Nanfe Joy Jatau: Budurwa mai digiri da ta cire girman kai take wankin mota

- Nanfe Joy Jatau wata matashiya ce mai mataukar kokari da rashin girman kai

- Duk da kammala digirinta da ta yi a jami’ar jihar jos, ta kama sana’ar wankin mota

- Ta yi kira ga ‘yan uwanta masu digiri da kada su saka wa kansu girman kai duk da kwalin da suka mallaka

Nanfe Joy Jatau matashiya ce da ta kammala karatun digirinta a jami’ar Jos a fannin wasan kwaikwayo. Amma ba kamar yadda aka san matan arewa ba, sai ta kama sana’ar wankin mota a garin Jos.

Nanfe ta bayyana cewa, bayan ta kammala karatun digirinta a fannin wasan kwaikwayo a jami’ar Jos, ta samu wani aiki da kamfanin inshora a Abuja. Wannan aiki da ta samu duk wata ana biyanta naira dubu ashirin.

Ganin yadda matsaloli suka yi mata yawa a Abuja, musamman matsalar tsadar rayuwa da wajen zama, sai ta ga aikin ba zai yuwu ba. Don haka sai ta bari.

Bayan ta bar wannan aikin, sai ta dawo Jos inda ta samu aikin koyarwa a wata makaranta. Ana biyanta albashin dubu biyar a duk wata.

KU KARANTA: Tirkashi: Bidiyon yadda wani Fasto yake yiwa mambobinsa bulala saboda sun daina zuwa coci

Ta kara da cewa, “Bayan da naga wannan aikin ba zai rike ta ba. Shi ne na samu yayana nace mishi ya taimakeni in bude wajen wankin mota. Yace zan iya wannan sana’ar? Shine ya bani kudi na bude wannan wajen wankin motocin. Yadda na kama wannan sana’ar kenan. Na kai wajen shekara daya da kama sana’ar.”

A karshe ta yi kira na musamman ga wadanda suka yi karatu a jami’a, da su cire girman kai, su kama sana’a maimakon su tsaya suna neman aikin gwamnati da ba ya samuwa yanzu a Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel