Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya dira Daura domin kaddamar da sabuwar jami'ar Sufuri

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya dira Daura domin kaddamar da sabuwar jami'ar Sufuri

Shugaba Buhari ya dawo Najeriya bayan 'yan sa'o'i a taron GECS da ya halarta a Malabo inda ya bayyana cewa za'a gina layin dogon iskar Gas daga jiha Kano zuwa kudancin Najeriya.

Mai magana da yawun Buhari, Garba Shehu, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki da yammacin nan inda yace:

"Shugaba Muhammadu Buhari ya dira mahaifarsa Daura, jihar Katsina bayan halartan taron kasashe masu fitar da iskar gas a Malabo, kasar Equatorial Guinea.

Buhari ya dira babban filin jirgin saman Umaru Musa Yar’Adua misalin karfe 4:20 na yamma kuma gwamnan jihar Katsina, Aminu Belli Masari ya tarbeshi.

Shugaba Buhari zai kaddamar da sabuwar jami'ar Sufuri dake Daura a ranar Litinin sannan ya kaddamar da sabuwar hanyar Kwanar Gwante dake Shargalle.

Kamfanin injiniyancin kasar Sin CCECC ce za ta gina jami'ar da za'a rika karantar da ilimin harkokin sufuri da bincike.

Buhari zai tafi Kaduna daga Daura ranar Talata."

Kalli hotunan:

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya dira Daura domin kaddamar da sabuwar jami'ar Sufuri

Yanzu-yanzu
Source: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel