Matashi dan garin Jos ya kera tsaleliyar mota tamkar a Turai (Hotuna da Bidiyo)

Matashi dan garin Jos ya kera tsaleliyar mota tamkar a Turai (Hotuna da Bidiyo)

Dan matashin Najeriya, haifaffen jihar Plateau, Jerry Isaac Mallo, ya hada wata tsalaliyar mota irinta na farko a Najeriya.

Injiniyan kuma shugaban kamfanin Bennie Technologies LTD, ya kaddamar da motar mai suna Bennie Purrie ranar Alhamis a Transcorp Hilton dake Abuja.

Yayinda yake da hira da manema labarai a tashar Channels TV, Mallo ya bayyana cewa ya himmatu wajen kera motoci ne saboda yan Najeriya da Afrika na son motoci.

Yace: "A Turai, mun samu labarin cewa ba kera mota bane kadai kalubale, sayarwa ma wani kalubalen ne; kuma Afrika aka sayar da yawancin wadannan motocin, shi yasa nace akwai kasuwa a nan."

Ya kara da cewa nahiyar Afrika na da dukkanin arziki kayayyakin hada wadannan motoci amma abin takaicin shine ba'a yi.

Jerry Mallo ya ce akwai matasa masu hazaka da dama a Najeriya amma ana asarar iliminsu tunda kasar bata dau aikin hannu da muhimmanci ba.

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai gwamnan jihar Plateaau, Simon Lalong.

Kalli hotunan da bidiyon:

Matashi dan garin Jos ya kera tsaleliyar mota tamkar a Turai (Hotuna da Bidiyo)
Matashi dan garin Jos ya kera tsaleliyar mota tamkar a Tura
Asali: Facebook

Matashi dan garin Jos ya kera tsaleliyar mota tamkar a Turai (Hotuna da Bidiyo)
Matashi dan garin Jos ya kera tsaleliyar mota tamkar a Turai (Hotuna da Bidiyo)
Asali: Facebook

KU KARANTA: Ba zamu daga zaben gobe ba - INEC ta mayarwa Dino Melaye martani

Matashi dan garin Jos ya kera tsaleliyar mota tamkar a Turai (Hotuna da Bidiyo)
Matashi dan garin Jos ya kera tsaleliyar mota tamkar a Turai (Hotuna da Bidiyo)
Asali: Facebook

Matashi dan garin Jos ya kera tsaleliyar mota tamkar a Turai (Hotuna da Bidiyo)
Gwamnan Plateau
Asali: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Kalli bidiyonsa:

Asali: Legit.ng

Online view pixel