Mun ciri tuta: An alanta Najeriya matsayin kasa mafi noman doya a duniya

Mun ciri tuta: An alanta Najeriya matsayin kasa mafi noman doya a duniya

Kungiyar abinci da aikin noma wato FAO ta alanta Najeriya matsayin kasa mafi noman doya yayinda kasar ke noman kashi 64 cikin 100 na doyan da akeci a duniya.

Sakataren din-din-din na ma'aikatar aikin noma da raya karkara, Dakta Mohammed Umar Bello, ya bayyana hakan ne a Abuja wajen taron wakshon wayar da kan al'umma kan noman doya.

Kungiyar Advocacy and Resource Mobilization Team ARMT ce ta shirya wakshon domin inganta abinci da tsaro a nahiyar Afrika ta yamma.

Mista Bello wanda ya samu wakilcin Diraktan aikin noman ma'aikatar, Frank Satumari Kudla, ya ce duk da cewa Najeriya ke noma kashi 64% na doyan duniya, ba ta cikin kasashen da ke fitar da doya kasashen wajen saboda rashin ingancin iri.

KU DUBA: Gwamnonin APC sun alanta Ganduje matsayin gwamna mafi aiki, ga jerin jihohin dake biye da Kano

Bello ya ce ma'aikatar ta jaddada bukatar inganta irin doya da kuma saukaka farashinsa saboda mano ma su samu cikin sauki domin nomawa.

Za ku tuna cewa a lokacin tsohon ministan aikin noma, Audu Ogbeh, tsakanin 2016 da 2019 an fara fitar da doyan Najeriya kasashen irinsu Amurka da Turai.

Daga baya an samu mishkila inda Doyan bai samun isa kasashen wajen sai ya kwashe watanni a tashohin ruwa kuma a wasu lokutan sun lalace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel