Innalillahi wa inna ilaihi raji’un: Mutane 9 sun halaka a sanadiyyar hadarin mota a Bauchi

Innalillahi wa inna ilaihi raji’un: Mutane 9 sun halaka a sanadiyyar hadarin mota a Bauchi

Akalla mutane tara ne suka gamu da ajalinsu a sanadiyyar wani mummunan hadarin mota daya auku a ranar Alhamis, 28 ga watan Nuwamba a kan babbar hanyar Bauchi zuwa Darazo, cikin jahar Bauchi.

Jaridar Punch ta ruwaito daga cikin mamatan akwai wata Uwa da jaririyarta, mace daya da kuma wasu fasinjoji maza guda 6, kamar yadda wata jami’ar asibitin koyarwa na jami’ar Abubakar Tafawa Balewa ta tabbatar.

KU KARANTA: Madallah: Sheikh Minista Pantami ya hana shugaba Buhari gaisawa da mata

“Na kirga gawarwaki guda 9 da aka kawo mana da safiyar nan, akwai Uwa da diyarta, wata budurwa da kuma maza guda shida.” Inji ta.

Ita ma hukumar kare haddura ta kasa reshen jahar Bauchi ta tabbatar da aukuwar hatsarin, amma ta ce mutane shida ne kawai suka rasu, kamar yadda kaakakinta, Rilwan Suleiman ya bayyana, inda yace wadanda suka mutu sun hada da Uwa da jaririyarta da maza hudu.

“A ranar 28 ga watan Nuwamba da misalin karfe 9:30 an safe mun samu rahoton hatsari daya hada da motoci guda biyu, Honda Hennesy dake dauke da mutane biyar da Volkswagen Sharon dake dauke da mutane 9.

“Hatsarin ya faru ne a lokacin da direban Hondan ya yi kokarin shigewa gaban motoci, inda ya yi taho mu gama da Sharon, jimillar mutane 14 ne hadarin ya rutsa dasu, nan take Sharon ta afka cikin daji, kuma mutane 6 suka mutu.” Inji shi.

Daga karshe Suleiman ya gargadi direbobi dasu guji tukin ganganci a kan hanya, saboda a cewarsa yawancin hadduran da ake samu suna faruwa a sanadiyyar rashin yin biyayya ga dokokin hanya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Online view pixel