An damke masu garkuwa da mutane 39 a jihar Kaduna

An damke masu garkuwa da mutane 39 a jihar Kaduna

Hukumar yan sandan Najeriya ta damke yan baranda 39 da suka addabi jihar kan laifuka da dama da ya hada da garkuwa da mutane, fashi da makami, damfarar yanar gizo da sauran laifukan.

Yayinda ake bayyana yan barandan ga duniya, kakakin hukumar yan sandan jihar, Yakubu Sabo, ya ce an samu nasarar damkesu ne ta hanyar hadin kai da al'umman gari.

Yace wasu daga cikin yan barandan sun dawo Kaduna buya daga Taraba ne bayan sun aikata ta'asan garkuwa da mutane a jihar.

A cewarsa, an samu manyan makamai a hannunsu wanda ya hada da AK47 goma, dogayen bindiga hudu, kananan bindigogi biyu, harsasai 154, motocin sata hudu da sauransu.

Wasu daga cikinsu sun bayyana cewa su aikata garkuwa da mutane a wurare daban-daban har da kisan jami'in dan sanda da wasu mutane biyu a kauyen Kangimi bayan karban kudin fansa.

A karshe, ya bayyana cewa an samu saukin barandanci da garkuwa da mutane a manyan hanyoyi, cikin gari da kauyuka.

A bangare guda, Wasu yan ta'addan Boko Haram sun kai hari Babban Gida, hedkwatan karamar hukumar Tarmuwa ta jihar Yobe a ranar Laraba, 27 ga Nuwamba, 2019.

Wani mazaunin Babban Gida, Alhaji Gidado, ya ce yan ta'addan sun fara kai hari mazaunin jami'an Soji kafin suka karasa wuraren ajiyan kayan abinci sukayi awon gaba da su.

Kwamishanan yan sandan jihar Yobe, Abubakar Sahabu, ya tabbatar da labarin inda yace DPO na Babban Gida ya laburta masa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel