Yarinya 'yar shekara 9 ta kashe kanta a Makurdi

Yarinya 'yar shekara 9 ta kashe kanta a Makurdi

Wata yarinya mai shekaru tara da haihuwa da kashe kanta a gidan masu rikon ta da ke Ankpa Quaters Extension a Makurdi na jihar Binuwai.

Daily Trust ta gano cewa lamarin ya faru ne a safiyar ranar Laraba inda aka gano gawar yarinyar a cikin bandaki.

Mai magana da yawun 'yan sandan jihar, DSP Catherine Anene, a ranar Alhamis ta tabbatar da afkuwar lamarin inda ta ce an sanar da su afkuwar lamarin ne misalin karfe 11.30 na safe.

Anene ta ce marigayiyar, "wata Abah Maria, mai shekaru 9 ta rataye kanta ne a bandaki."

Kakakin 'yan sandan ta kara da cewa an kai gawar yarinyar zuwa asibitin St. Theresa domin ajiye wa a dankin ajiyar gawarwaki yayin da ake cigaba da bincike.

DUBA WANNAN: 'Yan siyasa 3 da PDP za ta iya tsayarwa takara idan tana son karbe mulki a 2023

Anene ta kara da cewa kawo yanzu dai babu wanda aka kama game da afkuwar lamarin.

Majiyar Legit.ng da ta ziyarci gidan da aka ce yarinyar ta kashe kanta amma yaran da aka tarar a gidan sunyi bayyanin cewa mahaifiyarsu ne ya kamata tayi magana a kan lamarin amma ta fita.

Wasu mazauna unguwar da ke kusa da gidan sunyi ikirarin cewa an gano gawar yarinyar ne da zanni a daure a wuyanta, wadda hakan ke nuni da cewa akwai yiwuwar ta yi amfani da zanin ta sagale kanta ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel