Babbar magana: An kama basarake da laifin garkuwa da mutane a Kaduna

Babbar magana: An kama basarake da laifin garkuwa da mutane a Kaduna

Jami'an rundunar 'yan sanda a jihar Kaduna sun kama dakacin wani kauye a karamar hukumar Chikun na jihar da ake zargi da yi wa masu garkuwa da mutane aiki kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Dakacin kauyen yana daya daga cikin mutane 30 da ake zargi da laifuka da daban-daban da rundunar ta yi holen su a ranar Alhamis a cewar mai magana da yawun rundunar, DSP Yakubu Sabo Abubakar.

Sauran wadanda ake zargin sun hada da wata gungun masu garkuwa da mutane da suka kashe mutum biyu da suka sace bayan sun karbi kudin fansa naira miliyan 2.8 da kuma wasu mutane biyu da ake zargi da hannu cikin sace dalibai mata 6 da malamai biyu na Engravers College a Kaduna.

A yayin da ya ke jawabi kan wadanda ake zargin, mai magana da yawun 'yan sandan ya ce Dagacin Unguwan Luka, Samaila Luka yana aiki ne tare da masu garkuwa da mutanen ta hanyar basu bayyanai su kuma su rika bashi kasonsa bayan sun karbi kudin fansa.

DUBA WANNAN: 'Yan siyasa 3 da PDP za ta iya tsayarwa takara idan tana son karbe mulki a 2023

Ya ce masu garkuwa da mutanen da basaraken ke aiki da su sun kashe wane jami'in dan sanda bayan sun karbi kudin fansa.

Yayin amsa tambayar manema labarai, Luka ya musanta cewa yana yi wa masu satar mutanen aiki sai dai ya amsa cewa an bashi kudi sau biyu cikin lokuta uku da ya kaiwa masu satar mutanen kudin fansa.

A cewarsa, "Na taimaka wa mutane na kaiwa masu garkuwa da mutanen kudin fansa har sau uku. A karo na farko, sun bani N100,000, a karo na biyu sun bani N50,000 amma a karo na uku ba su bani ko sisi ba.

"Bani da masaniya kan dan sandan da masu garkuwa da mutanen suka kashe. Allah da 'yar sandan da aka sako su ne shaida na. A lokacin da na kai musu kudin fansan karo na uku, sun karba amma ba su saki dan sandan ba. Ni da dayan matan munyi kuka mun roke su amma ba su yarda ba, sun ce dansan ya saba zaginsu. A ranar sun karbi waya ta kuma ba su bani kudi ba," inji shi.

Luka ya ce bai san masu garkuwa da mutanen ba amma kuma bai taba fadawa 'yan sanda cewa sun bashi wani kaso cikin kudin fansar ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel