Mai alfarma Sarkin Musulmi ya bayyana yau a matsayin 1 ga watan Rabiul -Thani

Mai alfarma Sarkin Musulmi ya bayyana yau a matsayin 1 ga watan Rabiul -Thani

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya sanar da ranar Alhamis, 28 ga watan Nuwamba a matsayin ranar farko na watan Rabiul-Thani, ma’ana, 1/4/1441.

Legit.ng ta ruwaito wannan sanarwa ta fito ne daga kwamitin duba wata na majalisar koli ta musulunci dake karkashin shugabancin Sarkin Musulmi, inda kwamitin ta ce an yi katarin ganin jinjirin watan Rabiul Thani a daren Alhamis.

KU KARANTA: Cika shekaru 60 a rayuwa: Buhari ya yi ma Garba Shehu kyakkyawar shaida

Daga cikin jahohin da aka ga watan akwai wasu sassa na jahar Katsina, Kaduna, Bauchi, Sakkwato, Gombe da kuma babban birnin tarayya Abuja.

Daga karshe sanarwar ta karkare sanarwar da yin fatan Allah Ya baiwa al’ummar Musulmai ikon gudanar da dukkanin ibadun da suka rataya a wuyoyinsu kamar yadda addinin ya koyar, kuma Allah Ya karba, Ya saka musu da aljannar Firdausi.

A wani labarin kuma, majalisar zartarwar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta amince da kashe naira biliyan 19 domin ginin wasu manyan hanyoyi a jahar Kano, jahar Oyo da kuma babban birnin tarayya Abuja.

Ministan ayyuka, Babatunde Raji Fashola ne ya sanar da haka yayin da yake ganawa da manema labaru bayan kammala taron majalisar a ranar Laraba, 27 ga watan Nuwamba.

“An gabatar da takardar bukatar gina hanyar Igboho-Oloko-Agbonle a jahar Oyo, da hanyar Gulu zuwa garin Yaba a babban birnin tarayya Abuja da kuma hanyar Sharada-Madobi-Dan Baure a jahar Kano.

“Majalsar ta amince da kashe N7.29bn a kan hanyar dake jahar Oyo, N7.593bn a kan hanyar dake babban birnin tarayya Abuja da kuma N4.510bn a kan hanyar dake jahar Kano.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel