Arewa maso gabas ta fi sauran yankuna yawan mata masu fama da yoyon fitsari - Likita

Arewa maso gabas ta fi sauran yankuna yawan mata masu fama da yoyon fitsari - Likita

Shugaban asibitin magance ciwon yoyon fitsari ta kasa dake jihar Bauchi, Umar Ibrahim, ya bayyana cewa yankin Arewa maso gabashin Najeriya ta fi sauran yankunan kasar yawan mata masu fama da ciwon.

Ya bayyana hakan a hirar da yayi da manema labarai ranar Talata a garin Ningi inda yace an kafa asibitin ne don jinyan al'ummar jihohi shida amma mutane na zuwa daga dukkan sassan Najeriya.

Ciwon yoyon fitsari wanda akafi sani da VVF ciwon ne da ya shafi mata a lokacin haihuwa inda fitsari zai rika zuba ba tare sun sani ba.

DUBA NAN: Yanzu-yanzu: Rikici ya barke tsakanin yan Shi'a da yan sanda a Abuja, an kashe yar makaranta

Shugaban cibiyar yace: "Yankin Arewa maso gabas ce tafi kowace yanki yawan masu fama da wannan ciwon, musamman ta dalilin dadewa wajen nakuda, fyade da kuma rikice-rikicen Boko Haram."

"Cibiyar na jinyar akalla mutane 400 zuwa 500 a kowace shekara inda ake wasu a koda yaushe, wasu kuma sukan taru kimanin su 100 a lokaci daya."

A bangare guda, Hukumar sojin Najeriya ta ce tayar da bama-bamao ne babban kalubalen da hukumar ke fuskanta wajen yaki da ta’addancin yan tada kayar bayan Boko Haram.

Kwamandan injiniyoyin hukumar soji, Manjo Janar John Amalu, ya bayyanawa manema labarai a taron West Africa Social Activities (WASA) ranan Asabar a jihar Legas.

Yace: “Bama-bamai ne babban kalubale a yankin Arewa maso gabas kuma wannan babban cikas ne ga hukumar soji,”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel