Kiran ruwa: Cin mutuncin gwamna a Facebook ya jefa wani matashi a gidan yari
Wani ma’aikacin banki a Najeriya mai suna Michael Itok ya kira ma kansa ruwa sakamakon wani rubutun batanci da ya yi a kan gwamnan jahar Akwa Ibom, Udom Emmanuel, inda a yanzu haka yana gidan yari a daure.
Jaridar Premium Times ta ruwaito a ranar Talata, 26 ga watan Nuwamba ne hukumar tsaron farin kaya, DSS, ta gurfanar da matashi Itok a gaban kotun majistri, inda ake tuhumarsa da rubuce rubucen batanci a kan gwamnan.
KU KARANTA: Masu garkuwa da mutane sun sace babban hakimi a babban birnin tarayya Abuja
Tuhumar da ake ma Itok shi ne: “Kai Itok da wani abokinka a watan Oktoban shekarar 2019 a unguwar rukunin gidaje 1000 dake karamar hukumar Uruan, kun rubuta rubutun batanci a kan gwamnan jahar Akwa Ibom Emmanuel Udom da nufin bata masa suna, tare da sauran ma’aikatan fadar gwamnatin jahar.
“Wannan laifi ya saba ma sashi na 6(1) (f) na kundin dokokin tsaron cikin gida na jahar Akwa Ibom na shekarar 2009.”. A yanzu haka dai an garzaya da Itok zuwa gidan maza dake garin Uyo, babban birnin jahar Akwa Ibom.
Wani jami’in bankin Prudential Microfinance Bank, bankin da Itok ke aiki ya bayyana cewa da misalin karfe 7:30 na safiyar ranar 8 ga watan Oktoba ne jami’an DSS suka dauke Itok daga bankin.
Da yake jami’in bankin yace baya nan lokacin da aka kama Itok, amma ya bar masa takarda dauke da sako kamar haka; “Ba lallai bane na iya isar da sakon nan baki da baki, amma idan kuka ji shiru ban dawo wurin aiki ba, ko kuma baku gan ni ba, ku sani yaran Udom ne suka kama ni.”
Wannan dai ba shi ne karo na farko da ake kama matasan dake rubuce rubuce a kan gwamnoni da manyan yan siaysa ba, ko a yanzu haka akwai wani dalibin jami’ar Bayero ta Kano dake daure a gidan yari a dalilin wani rubutu da ya yi a kan wani dan majalisan dokokin jahar Kano.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng