Jama'an da ke zaune a Legas kadai sun fi yan kasar Holan yawa - Firam Ministan Holand

Jama'an da ke zaune a Legas kadai sun fi yan kasar Holan yawa - Firam Ministan Holand

Firam ministan kasar Holand, Mark Rutte, ya ce girman kasa da yawan mutanen Najeriya ya bashi tsoro.

Rutte ya siffanta Najeriya matsayin kasa mai girma sosai tunda al'ummar jihar Legas kadai sun fi dukkan jama'ar kasar Holand yawa.

Ya yi magana ne bayan ganawarsa da shugaba Muhammadu Buhari a Abuja.

Rutte ya kawo ziyaran kwana biyu Najeriya ne domin karfafa alakar diflomasiyya da kasuwanci da Najeriya.

A cewarsa: "Najeriya na da girma sosai. Ina farin cikin zuwa Najeriya. Wannan shine karo na farko da zan kawo ziyara Najeriya kuma ina matukar farin ciki."

"Duk abinda ka gani a kasar nan na da firma. Ta fi kasar Holand girma sau ashirin. Mutanen da ke zaune a Legas kadai sun al'ummar kasata yawa."

Shugaba Muhammadu Buhari da Firam ministan Holand, Mark Rutte sun gana a Abuja a yau Talata.

Sun tattauna kan kasuwanci tsakanin kasashen biyu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel