Wani kauye a jihar Kano da bindiga ko wuka ba sa cutar da dan garin

Wani kauye a jihar Kano da bindiga ko wuka ba sa cutar da dan garin

- Wani rafi a kauyen jihar Kano mai suna Tanagar na da tarin abubuwan mamaki

- Mazauna kauyen na amfani da ruwan rafin don aiyukan yau da kullum kuma a matsayin magani

- Wani babban abun mamaki shine, yadda wuka, kibiya, bindiga da duk wani karfe baya kama ‘yan kauyen

Abun al’ajabi ba ya karewa a duniya. Ubangiji ya halicci wani rafi mai tarin abun mamamki a wani kauye da ake kira da Tanagar da ke jihar Kano.

A kauyuka da dama ana samun rafi, amma wannan rafin ba kowanne iri bane. Kamar yadda mazauna kauyen suka sanar, ruwan rafin nan ya na musu amfani mai tarin yawa. Daga cikin amfanin ruwan rafin nan kuwa ya hada da kariya daga harbin bindiga.

Mazauna garin Tanagar kan yi amfani da ruwan wajen aiyukansu na yau da kullum. Amma sun tabbatar da cewa, ruwan wannan rafin na da gardin da ya wuce na rijiya ko na tuka-tuka. Amma kuma baya kashe kishi.

A lokacin da ba damina ba, ruwan rafin yana karewa, amma ana tona kasar rafin kadan, a kan samu ruwa mai yawa wanda zai isa mutum yin al’amuran rayuwa.

KU KARANTA: Ba harkar fim ce ta hanani zaman gidan aure ba - Inji Fati KK bayan an ganta a wani sabon fim

Ba wai harbin bindiga kadai ba, duk wanda ya sha ruwan rafin nan karfe baya kamashi. Wani mazaunin kauyen Tanagar ya ce, a lokutan bikin al’adar kauyen, yara kan guntsa kalanzir a baki su hura wa wuta sama don nishadi.

A kan samu akasi inda kalanzir din ke wucewa wasu, amma shan ruwan wannan rafin kan kasance magani ga wadanda suka hadiye kalanzir din.

Wani mazaunin garin ya bayyana yadda yaran garin ke yin wasa da kibiya, mashi ko dai wasu karafa masu tarin hatsari, amma ba ya illatasu saboda shan ruwan wannan rafin mai tarin abun mamaki.

Ana yi wa garin kirari da tanagar kan tudu, garin magajin Malam.

Mazauna garin kan ba wa mutanen da ba ‘yan garin ba maganin karfen, kuma yana aiki ba kadan ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel