Yadda wasu 'yan bindiga 8 suka yi wa jirgin sama fashi

Yadda wasu 'yan bindiga 8 suka yi wa jirgin sama fashi

- Wasu 'yan bindiga takwas sun afkawa jirgin sama a Papua New Guinea sunyi awon gaba da kayayyakin da jirgin ke dauke da shi

- 'Yan bindigan sun afkawa jirgin ne a lokacin da matukin jirgin ya yada zango a wani karamin gari domin kara mai

- 'Yan bindigan sun tilastawa matukin jirgin zuwa wani karamin filin jirgi da aka dena amfani da shi sannan suka sace kayayyakin da jirgin ke dauke shi

Wasu mutane dauke da bindigu sun afkawa wani jirgin sama na haya a Papua New Guinea a ranar Talata inda suka tilastawa matukin jirgin ya kai su wani filin saukan jirage da aka dena amfani da shi sannan suka sace kayayyakin da jirgin ke dauke da su.

Tropicair ta shaidawa AFP cewa mutane takwas dauke da bindigu sun tarar da jirgin ne a lokacin da ta sauka a Gasmta domin kara mai a wani tsibirin New Britain inda suka tilastawa matukin jirgin ya sake tashi zuwa wani wani wurin.

Mai magana da yawun kamfanin jiragen saman da ya yi tsokaci kan afkuwar lamarin ya ce babu fasinjoji a cikin jirgin.

DUBA WANNAN: Hotunan wasu takalman Buhari da ya dauki hankulan 'yan Najeriya a Twitter

Matthew Brutnall ya ce, "Bayan da ya isa karamin filin saukan jiragen, 'yan bindigan sun sace kayayyakin da ya ke dauke da su a jirgin kuma suka tsere."

"Matukin jirgin bai samu rauni ba kuma ba a lalata jirgin saman ba" kuma tuni jirgin ya dawo Port Moresby.

Mahukunta a Royal Papua ta New Guinea sun tabbatar da afkuwar lamarin inda suka ce an fara gudanar da bincike don gano wadanda suka aikata fashin kamar yadda The Punch ta ruwaito.

A halin yanzu dai ba a bayyana irin kayayyakin da 'yan bindigan suka sace daga cikin jirgin ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel