Tirkashi: Fasto ya shiga tsaka mai wuya bayan matar da ya gayyata taje gidanshi ta mutu jim kadan bayan ya kammala zina da ita

Tirkashi: Fasto ya shiga tsaka mai wuya bayan matar da ya gayyata taje gidanshi ta mutu jim kadan bayan ya kammala zina da ita

- Wani Fasto ya shiga tsaka mai wuya bayan da budurwarshi ta mutu jim kadan bayan sun gama lalata bayan ta kai mishi ziyarar ba zata

- ‘Yan sandan sun gano Faston ne bayan da aka bi hirarsu a Facebook tare da bin diddigin kiraye-kirayen wayar da ta dinga ranar da ta bar gida

- Faston ya bayyana yadda ta kai mishi ziyara amma ta rasu, tsoron kada asirin sa ya tonu ne ya sa ya yadda gawarta a gefen titi

Runduna ta musamman ta hukumar ‘yan sandan jihar Osun, ta binciko wani Fasto da yayi ikirarin wata mata mai suna Yemisi ta mutu a dakinshi bayan da suka gama lalata.

Yemisi mai shekaru 52, 'yar asali karamar hukumar Akure ce da ke jihar Ondo. Ta kaiwa Fasto Martey ziyara ne bayan da suka shirya hakan ta kafar sada zumunta na Facebook.

Yemisi ta bar gida a ranar 28 ga watan Yuli amma tayi batan dabo, don har ‘yan uwanta basu san inda ta nufa ba. Tuni dai suka garzaya tare da kai rahoton bacewar ‘yar uwarsu ga runduna ta musamman ta ‘yan sandan jihar .

Bayan dogon binciken da ya dauki kusan watanni uku, jami’an ‘yan sandan sun bi diddigin inda ta je na karshe tare da wanda ta dinga waya dashi da kuma hira a Facebook. Babu tantama kuwa suka cafke wani Fasto mai shekaru 42 a Benin City dake jihar Edo.

Kamar yadda Faston ya sanar da ‘yan sandan, ya ce sun hadu da Yemisi a kafar sada zumunta ta Facebook. Sun karbi lambar wayar juna kuma ita ta matsa masa a kan tana so ta ziyarceshi.

KU KARANTA: Bayan ya gama wahalar budewa matarsa sabon shagon sayar da kaya, ranar da ya fara kawo mata ziyara ya tarar da ita da katon gardi suna lalata a ciki

A ranar 28 ga watan Yuli, Yemisi ta iso Benin City inda ta kirashi ya dauketa daga tashar mota. Bayan ta gama hutawa ta ci abinci sannan suka fara tattauna yadda zasu tsara rayuwarsu.

Faston ya sanar da ita cewa, ba zai iya aurenta ba saboda ta tsufa, shi kuwa yana bukatar haihuwa. Ta ce mishi sun dace, saboda yana rubuta litattafan addini ita kuwa ta iya tace rubutu. Kuma a kan maganar haihuwa, da izinin Ubangiji zasu haihu.

Bayan dare ya raba suka sadu da juna. Amma kafin wayewar gari, ya duba ya ga ta mutu. Tsoron abinda zai kai ya kawo yasa ya ja gawarta zuwa gefen titi. Daga nan kuwa bai san inda aka yi da gawar ba, duk da ya ga mutanen anguwar sun taru a kanta.

Hukumar ‘yan sandan na cigaba da bincike don samo gawar tare da gano menene musabbabin mutuwarta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel