Tsohuwa yar shekara 82 ta yiwa matashi dukan da sai da aka kaishi asibiti

Tsohuwa yar shekara 82 ta yiwa matashi dukan da sai da aka kaishi asibiti

Wata tsohuwa yar shekara 82 mai suna, Willie Murphy, ta ladabtar da wani matashin da yayi kokarin shiga gidanta karfi da yaji har da balla mata kofa.

Willie Murphy ta lallasa shi har sai da aka garzaya da shi asibti.

Tsohuwar ta bayyana cewa yayinda take kokarin kwanciya a gidanta dake Rochester, New York, Amurka misalin karfe 11 na dare, sai taji ana buga mata kofa da karfi.

Tace wani mutumi na waje yana iwun a kira masa jami'an asibiti saboda bashi da lafiya. Sai ta kira yan sanda domin su kaishi asibiti tun da abinda yake bukata kenan amma sai mutumin ya fara fushi saboda ta hanashi shiga gidanta.

Tsohuwa yar shekara 82 ta yiwa matashi dukan da sai da aka kaishi asibiti

Tsohuwa yar shekara 82 ta yiwa matashi dukan da sai da aka kaishi asibiti
Source: Facebook

KU KARANTA: Wasu marasa kishin kasa na yi mini zagon kasa - Sheikh Isa Pantami

Kawai sai taji wani kara a bakin kofa, ashe ya balla kofarta zai shiga karfi da yaji.

Tace: "Kawai sai na dauki teburi na maka masa sai da ta karye. Da fadi kasa kuwa, ban daina dukansa ina takashi."

"Sai na garzaya cikin kicin na dauki kwalban sabulu na watsa mai a fuska. Yayinda yake kokarin tashi, sai na dauki tsintsiya na rika buga mai har sai da ya fara kokarin guduwa. Gaskiya na lallasa mutumin nan sosai."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel