Gwamna Matawalle ya rike min kudin fansho da alawus - AbdulAziz Yari

Gwamna Matawalle ya rike min kudin fansho da alawus - AbdulAziz Yari

Tsohon gwamnan jihar Zamfara, AbdulAziz Yari, ya bayyana cewa magajinsa, gwamna Bello Matawalle, ya hanashi kudin fansho da alawus dinsa a matsayin tsohon gwamna kamar yadda dokar jihar ta tanada.

A wasikar da ya aikawa gwamnan, Abdulaziz Yari, ya bukaci gwamna Matawalle ya biyashi kudaden saboda babu wani dalilin da zai sa ya rike masa kudi.

Yari ya ce tun da ya sauka daga mulki, sau biyu kacal aka biyashi kudin kula da kansa na N10m a wata.

Ya ce dokar jihar ta tanadi baiwa tsaffin gwamnoni, mataimakan gwamnoni, tsaffin kakakin majalisa, da mataimakansu, alawus a ko wani wata.

DUBA NAN Hotunan bikin daurin auren matashin da ya auri yan mata uku rana daya

A cewarsa: "Ina son jawo hankalinka kan wannan dokar da aka gyara kuma aka rattaba hannu ranar 23 ga Maris, 2019."

"Dokar ta tanadi cewa daga cikin abubuwan da tsohon gwamna ya cancanta shine alawus na wata milyan goma (N10,000,000) da fansho daidai kudin albashin da yake dauka lokacin da yake mulki."

"Saboda haka, ina mai sanar da kai cewa tun lokacin da wa'adi na ya kare a ranar 29 ga Mayu, 2019, sau biyu kadai aka biyani kudin; watan Yuni da Yuli kuma ba'a biyani kudin fanshon watan Yuni ba."

Gwamna Matawalle ya rike min kudin fansho da alawus - AbdulAziz Yari
Gwamna Matawalle ya rike min kudin fansho da alawus - AbdulAziz Yari
Asali: Facebook

A bangare guda, Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Zamfara ta musanta zargin da ake yiwa tsohon gwamnan jihar, AbdulAziz Yari, cewa yana goyon bayan yan bindigan da suka addabi jihar tun lokacin da yake gwamna.

A makon jiya, wasu yan bindiga sun hallaka akalla mutanr 18 a garin Karaye dake karamar hukumar Gummi ta jihar Zamfara.

Gwamnan jihar, Bello Matawalle, ya tuhumci magabacinsa, AbdulAziz Yari, da laifin yiwa yunkurin kawo zaman lafiya zagon kasa da cika duk lokacin da ya ziyarci jihar.

Gwamnan ya yi barazanar daure gwamnan idan ya sake shiga jihar Zamfara ya tayar da tarzoma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel