Yari mai ilimin addini ne kuma mai tsoron Allah - APC ta mayarwa Matawalle martani

Yari mai ilimin addini ne kuma mai tsoron Allah - APC ta mayarwa Matawalle martani

Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Zamfara ta musanta zargin da ake yiwa tsohon gwamnan jihar, AbdulAziz Yari, cewa yana goyon bayan yan bindigan da suka addabi jihar tun lokacin da yake gwamna.

A makon jiya, wasu yan bindiga sun hallaka akalla mutanr 18 a garin Karaye dake karamar hukumar Gummi ta jihar Zamfara.

Gwamnan jihar, Bello Matawalle, ya tuhumci magabacinsa, AbdulAziz Yari, da laifin yiwa yunkurin kawo zaman lafiya zagon kasa da cika duk lokacin da ya ziyarci jihar.

Gwamnan ya yi barazanar daure gwamnan idan ya sake shiga jihar Zamfara ya tayar da tarzoma.

Kakakin APC a jihar, Ibrahim Gidangoga, ya bayyanawa manema labarai a Gusau cewa wannan zargi ba gaskiya bane cewa "Yari yana tattaunawa da yan bindiga kuma yana daukan nauyin hare-haren da suke kaiwa yankunan jihar."

Ya ce "tsohon gwamnan mutumin kirki ne, wanda ake ganin girmansa kuma babbar manufarsa itace inganta rayuwan mutanensa."

Duk da cewa hukumar EFCC na binciken Yari, Ibrahim Gidangoga, ya ce "Yari mutum ne mai rikon addini sosai kuma mai ilimin addinin mai zurfi kuma ya san hukuncin hada baki wajen hallaka rayuwa mutum."

"Saboda haka, babu yadda mai ilimin addini kuma mai riko da addini kaman tsohon gwamnan wanda ya shugabanci jihar na tsawon shekaru takwas zai rage mutuncinsa wajen daukan nauyin yan bindiga wajen kashe mutane."

Kakakin APC ya ce sabanin zargin da gwamna Matawalle ke yi, Yari bai shiga wani gari a jihar Zamfara ba tun da ya bar mulki face mahaifarsa Talata Mafara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel