Pantami ya yi magana kan dokar hana kai man fetur garuruwan kusa da iyakokin Najeriya

Pantami ya yi magana kan dokar hana kai man fetur garuruwan kusa da iyakokin Najeriya

Ministan sadarwa, Isa Pantami, ya shawarci hukumar kwastam ta kasa da ta dage dokar hana kai man fetur garuruwan da ke kusa iyakokin kasar nan. Hakan ya zama babban kalubalen da ma'aikatarsa ke fuskanta.

Kamar yadda takardar da ta samu jaridar Premium Times a ranar Juma’a, wacce mai magana da yawun minstan, Uwa Suleiman ta fitar, ta ce hakan zai bayar da dama kamfanonin sadarwa su tayar da injinan wutansu don samar da ayyukansu ga ‘yan Najeriya.

Babu dadewa kasar Najeriya ta rufe iyakokinta don shawo kan matsalar shigowa da haramtattun abubuwa, tare da bunkasa samar da kayayyakin amfani a cikin kasar nan. Iyakokin za su kasance a rufe ne har zuwa watan Janairu na 2020.

Hukumar kwastam ta kasa ta sanar da hana kai man fetur garuruwan da ke da kusancin kilomita 20 daga iyakokin kasar nan.

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa fusatattun shugabannin APC suka nema Oshiomhole ya sauka kujerarsa

A kalla iyakoki 57 Najeriya ta rufe tun daga watan Augusta a yunkurinta na rage shigo da kayayyaki daga kasashen ketare zuwa kasar nan.

Kamfanonin sadarwan sun ja kunnen cewa, wasu yankunan kasar nan zasu fuskanci kalubale ta fannin sadarwa, sakamakon hana kai mai yankunan da suke da makwabtaka da iyakokin kasar nan da hukumar kwastam ta kasa ta yi.

Kungiyar kamfanonin sadarwan ta sanar da cewa, za a rufe babban ofishin sadarwa da ke yankin Calabar saboda rashin man tada inijnansu. Umarnin hukumar kwastam din ta zama babbar barazana ga kamfanonin sadarwa na kasar nan.

“Korafe-korafe masu yawa sun iso ofishin ministan a kan zargin jami’an kwastam, ballantana wadanda ke garuruwan iyakokin kasar nan, a kan hana tankokin man fetur shiga garuruwan," in ji takardar.

"Hakan kuwa na kawo rashin man fetur din tada injinan aiyukan kamfanonin sadarwa da ke garuruwan. Haka zai zama babban kalubale ga tsaron kasa da kuma cigaban tattalin arziki, wanda bai kamata a zuba ido a kalli faruwar hakan ba,” takardar ta kara da cewa.

Pantami ya yi kira ga gwamnonin jihohin da abun ya shafa da su dau mataki wajen tabbatar da an shawo kan wannan matsalar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel