Innalillahi: Wata mata ta bayyana yadda take dafawa mutane abincin sayarwa da jinin al'ada

Innalillahi: Wata mata ta bayyana yadda take dafawa mutane abincin sayarwa da jinin al'ada

- Wata mata mai karamin gidan abinci ta bayyana yadda ta ke amfani da ruwan gabanta, ruwan wankan gawa da jinin al’adarta don hada sanwar girkin abincin siyarwan ta

- Ta bayyana hakan ne jim kadan bayan da ta haukace, ta fara yaga kayan jikinta tare da zayyano duk sharrikan da ta shirya don jawowa kanta kasuwa

- A cewarta, hikimarta ta yin hakan kuwa shine jawo kwastomomi tare da tattara duk arzikin wadanda suka ci abincin nata don habaka kanta da kasuwancinta

Wata mata mai karamin gidan cin abinci irin wanda ake kira da ‘buka’ ta bayyana yadda take amfani da ruwan gabanta, ruwan wankan gawa da kuma jinin al’adarta wajen hada sanwa don jawo kwastomomi.

Kamar yadda ganau ba jiyau ba ya bayyana, mai abincin mai suna Happiness, ‘yar asalin jihar Akwa Ibom ta haukace ne a wajen cin abincin nata. Wajen na nan a Aleto da ke karamar hukumar Eleme da ke Fatakwal cikin jihar Rivers.

Budurwar ta haukace ne tare da yaga kayan jikinta inda take bayyana sharrin da ta dinga shiryawa don cigaban kasuwancinta. Kamar yadda ta fada, ta ce tana hada ruwan gabanta, ruwan wankan gawa da kuma jinin al’adarta don hada abincin siyarwan.

KU KARANTA: Binciken masana: Kwakwalwar mata ta fi ta maza aiki da kaifin tunani

Ta ce, tana hakan ne don jawo kwastomoni wadanda take tattara “arzikinsu” don habakar kanta da na kasuwancinta. Bayan gama fadin sharrikan da ta dinga shiryawa, ta yaga kayan jikinta tare da fara yawo tsirara. Babu ko shakka, haukacewa ta yi.

Labarin bayanin da ta dinga yi game da abincinta ya kewaye yankin, kuma wasu daga cikin kwastomominta, wadanda akasarinsu ;yan achaba ne, sun fusata tare da jibgarta. Babu dadewa jami’an ‘yan sanda suka bayyana inda suka yi awon gaba da ita.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel