Yan bindiga sun bindige basaraken gargajiya a jahar Katsina

Yan bindiga sun bindige basaraken gargajiya a jahar Katsina

Wani basaraken gargajiya da gungun miyagu yan bindiga suka kai masa hari a kauyen Yandaka na karamar hukumar Batsari ta jahar Katsina ya rigamu gidan gaskiya a ranar Alhamis, 21 ga watan Nuwamba a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano, AKTH Kano.

Jaridar Katsina Post ta ruwaito basaraken gargajiyan, wanda shine dakacin kauyen Yandaka, Alhaji Shehu Iliyasu Ruma ya rasu ne sakamakon raunin daya samu a dalilin harbin da yan bindigan suka yi masa a kai da hannu.

KU KARANTA: Yan bindigan dake fitinar jahar Zamfara abokanka ne, ka sansu – Yari ga Matawalle

A wannan rana da yan bindigan suka kai farmaki kauyen Yandaka cikin karamar hukumar Batsari sun tattara iyalan dakacin da suka hada da matarsa da yaransa guda uku, sa’annan daga bisani suka dirka masa harsashi a kai da hannu.

A dalilin raunin daya samu a yayin harin ne aka garzaya da shi zuwa asibitin AKTH dake Kano domin samun kulawa, sai dai kash! Rai ya yi halinsa, inda ya rasu ya bar mata guda daya da yaransu guda 10.

A wani labarin kuma, wasu gungun yan bindiga sun kaddamar da hari a karamar hukumar Mangu inda suka kashe shugaban kungiyar Fulani makiyaya na Miyetti Allah reshen karamar hukumar, Sa’adu Musa Julde.

Yan bindigan sun kaddamar da harin ne a daren Laraba, 20 ga watan Nuwamba, inda suka bindige Ardo Sa’adu Musa Julde, sa’annan suka tsere cikin daji ba tare da an kama ko mutum daya daga cikinsu ba.

Wani ma’abocin kafar sadarwar zamani ta Facebook, wanda kuma shine shugaban kungiyar Miyetti Allah reshen jahar Filato, Malam Muhammad Nura Abdullahi ya tabbatar da kisan Ardo Sa’adu a shafinsa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel