Buge jami'an NSCDC da mota: Shehun Borno ya nemi afuwan jami'in tsaron da dansa ya doke

Buge jami'an NSCDC da mota: Shehun Borno ya nemi afuwan jami'in tsaron da dansa ya doke

Mai martaba Shehun Borno, Abubakar Ibn Umar El-Kanemi, da kansa ya nemi afuwar jami'an hukumar NSCDC, Usman Bakari, da 'dan gidansa, Kashim El-Kanemi, ya doke da mota a ranar Asabar.

Daya daga cikin fadawan Shehin ya bayyanawa PRNigeria cewa mai martaba ya baiwa jam'in tsaron N100,000 domin sayen magani.

Bafaden ya ce mai martaba EL-Kanemi ya nuna bacin ransa kan rahoton da bidiyon abinda ya faru kuma ya tura wakilan fada gidan jami'in tsaron domin neman uzurinsa da bashi hakuri.

Ya ce Shehun bai samu labarin abinda ya faru ba sai lokacin da ya ga faifan bidiyon a soshiyal midiya.

DUBA NAN Buhari ya shiga ganawa da shugabannin majalisun dokokin jihohin Najeriya 36

Bafaden wanda aka sakaye sunansa yace: "Shehun Borno ya siffanta wannan tsautsayi a matsayin abinda ke da hadari ga rayuwar jami'in NSCDC kuma abin ne wanda kan iya bata sunan mai martaba Shehun Borno."

Mun kawo muku rahoton cewa Haifaffen dan mai martaba Shehun Borno, Kashim Abubakar - ElKanemi, ya doke jami'in hukumar NSCDC a birnin Maiduguri yayinda ake wasan mota.

PRNigeria ta bada rahoton cewa matashin ya make, Usman Bakari, jami'in NSCDC dake aiki ofishin hukumar dake Maiduguri.

A cewar PRNigeria, wannan hadari ya faru ne misalin karfe 5:30 na yamma a farfajiyar Ramat dake Maiduguri ranar Asabar, 16 ga Nuwamba, 2016.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel