Tashin hankali: Wasu matasa sun rabawa yan gidan biki lemu lode da kwaya a Katsina

Tashin hankali: Wasu matasa sun rabawa yan gidan biki lemu lode da kwaya a Katsina

Wasu bata garin matasa sun bugar da bakin Walima a taron bikin inda suka raba lemu bayan sun zuba kwaya mai bugarwa wanda ya kai ga mutuwan mutum daya a karamar hukumar Batagarawa ta jihar Katsina.

Daya daga cikin matasan, Mudassiru Tanimu, ya shiga hannun hukumar yan sanda amma abokinsa Nafi'u Umar ya arce.

Wannan na kunshe cikin jawabin da kakakin hukumar yan sandan jihar SP Gambo Isah ya saki inda yace:

"A ranar 17/11/2019 misalin karfe 09:00hrs, hukuma ta damke wani Mudassiru Tanimu, mai shekaru 18 da haihiwa a kauyen Barhim, karamar hukumar Batagarawa a jihar Katsina wanda ya hada baki da wani Nafiu Umar suka hada lemu da kwayoyi kuma aka rabawa baki a waliman biki."

"Sakamakon haka, wani Iliyasu Musa da Rabiu Sani suka sha lemun kuma tuni sun fita daga hayacinsu."

"An garzaya da su babbar asibitin Katsina inda aka tabbatar da mutuwar Iliyasu kuma Rabiu na cikin maye."

"Abin zargin (Muddasur) ya amince da zargin aikatan laifin."

A bangae guda, Wata mata mai suna Risikat Olabintan yar jihar Ogun ta jefa sabon jaririn da ta haifa cikin Masai kawai saboda yara sunyi mata yawa.

Tace: "Ina da yara biya da nike wahalan ciyarwa kullum. Mijina ya tafi ya bar ni da su. Saboda haka bana bukatan wani yaron shi yasa ya jefa shi cikin Masai ina haifan shi."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Online view pixel