Yan Boko Haram sun bankawa asibiti wuta a jihar Yobe

Yan Boko Haram sun bankawa asibiti wuta a jihar Yobe

Wasu yan kungiyar tada kayar bayan Boko Haram sun bankawa wata asibitin Ngurbuwa dake karamar hukumar Gujba ta jihar Yobe. Channel TV ta ruwaito.

Wani mazaunin garin, Mohammed Mohammed, ya yi bayanin cewa yan ta'addan sun dira garin ne cikin mota kirar Hilux suna harbin kan mai uwa da wabi kafin suka bankawa asibitin wuta.

An samu labarin cewa ba'a dade da gyara asibitin ba saboda a farkon shekarar nan kwamitin majalisar dinkin duniya UNDP ta bada sabbin kayayyakin kiwon lafiya ga asibitin.

Yan Boko Haram sun bankawa asibiti wuta a jihar Yobe
Yan Boko Haram sun bankawa asibiti wuta a jihar Yobe
Asali: Facebook

Yan Boko Haram sun bankawa asibiti wuta a jihar Yobe
Yan Boko Haram sun bankawa asibiti wuta a jihar Yobe
Asali: Facebook

A wani labarin daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya saya ma rundunar Sojin saman Najeriya sabbin jiragen yaki na zamani guda 18 domin kara mata karfi a yakin da take yi da yan ta’adda, wanda a yanzu haka ake tsumayin isowarsu Najeriya.

Babban hafsan sojan sama, Saddique Abubakar ne ya bayyana haka a yayin bude taron samun horo na kwanaki biyu wanda rundunar ta shirya ma jami’anta a kan dabarun sadarwa a babban birnin tarayya Abuja, a ranar Talata.

KU KARANTA: Shegiyar uwar: Wata mata ta jefar da sabon jaririnta cikin Masai

Da yake jawabi a yayin bude taron, Saddique, wanda ya samu wakilcin shugaban sashin mulki na rundunar Sojan sama, Kingsley Lar, ya bayyana cewa rundunar ta sayi wadannan jirage 18 ne sakamakon goyon bayan da take samu daga gwamnatin tarayya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel