Bamu gana da El-Zakzaky ba tun da ya dawo daga Indiya - Iyalansa

Bamu gana da El-Zakzaky ba tun da ya dawo daga Indiya - Iyalansa

Daya daga cikin iyalan shugaban kungiyar mabiya akidar Shi'a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, ya ce rabon da su gana da mahaifinsu tun lokacin da ya dawo jinya daga kasar Indiya.

Dan gidan Zakzaky, Badamasi Ya'akub, ya bayyana a jawabin da ya saki ranar Talata cewa basu hadu da shugabansu ba tun dawowarsa daga Indiya.

Ya sakin jawabin ne domin mayar da martani ga hukumar DSS da suka yi jawabi a baya.

Yace: "Babu wanda yayi magana ta wayar tarho da Sheik Zakzaky tun lokacin da ya dawo daga tafiyar jinya zuwa Indiya."

"Bai samun karanta jaridu a kowani lokaci. Ina da tabbacin cewa rabonshi da ya kalli Talabijin tun a gidansa a Disamba 2015 da Sojojin Najeriya suka kai hari gidansa suka rusa."

"Kan maganan cewa yana atisaye kuma yana jin dadi, ko akwai gaskiya cikin wannan, toh Zakzaky da kansa ke biya."

"Sai mun sha wahala da biyan makudan kudi kafin mu iya aika musu magani."

Gwamnatin Tarayya tayi zargin cewa shugaban kungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN), Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, na da manufar son kafa kasar musulunci a Najeriya.

FG tace malamin yana da cikakken goyon bayan gwamnatin kasar Iran don cimma wannan manufar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel