Yanzu-yanzu: 'Dan Shehun Borno ya make jami'in tsaro wajen wasan mota (Bidiyo da Hotuna)

Yanzu-yanzu: 'Dan Shehun Borno ya make jami'in tsaro wajen wasan mota (Bidiyo da Hotuna)

Haifaffen dan mai martaba Shehun Borno, Kashim Abubakar - ElKanemi, ya doke jami'in hukumar NSCDC a birnin Maiduguri yayinda ake wasan mota.

PRNigeria ta bada rahoton cewa matashin ya make, Usman Bakari, jami'in NSCDC dake aiki ofishin hukumar dake Maiduguri.

A cewar PRNigeria, wannan hadari ya faru ne misalin karfe 5:30 na yamma a farfajiyar Ramat dake Maiduguri ranar Asabar, 16 ga Nuwamba, 2016.

A bidiyon, an ga inda aka ga yaran manyan masu kudin Borno suna wasa da manyan motoci karkashin wata daba mai suna “Yarwa Squad”.

Wani mai idon shaida ya bayyanawa PRNigeria ranar Litinin cewa yayinda jami'in NSCDC ya ke kokarin hanasu, sai 'dan Shehun Borno ya dokeshi da mota.

Yanzu-yanzu: 'Dan Shehun Borno ya make jami'in tsaro wajen wasan mota (Bidiyo da Hotuna)
Bakari
Source: Facebook

Yace: "Bakari ya zo yana rokanmu cewa mu daina wasan amma wasu matasa suka fara zaginsa suna dura masa ashar."

"Wasu daga cikin matasan na cewa Maiduguri tasu ce, kuma suna da hakkin duk abinda suka ga dama"

"Kawai sai 'dan Shehun Borno ya juya da motar da gug kuma ya make jami'an tsaron."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel