Ana ga wata, ga wata: An yi bukin radin sunan awakai biyu, Afnan da Hanifa

Ana ga wata, ga wata: An yi bukin radin sunan awakai biyu, Afnan da Hanifa

Hausawa suka ce kowa da kiwon da ya karbe shi, haka zalika, wai sa kai ya fi bauta ciwo. A ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamba, wani abun al'ajabi ya faru a unguwar Hardo da ke titin Railway, a cikin kwaryar jihar Bauchi, inda aka yi bukin radawa wasu awakai guda biyu suna, Afnan da Afra.

Hajiya Fatima wacce ke da awakin, ita ce ta shirya wannan gagarumin buki, inda ta gayyato kawayenta da abokan arziki, tare da gayyato makidin zamani (D.J) domin taya su murnar wannan rana ta radin sunan awaki biyu da uwar garkenta ta haifa.

Wakilin Legit TV Hausa a jihar Bauchi, Sani Hamza Funtua, ya halarci gidansu Hajiya Fatima, a lokacin da ake gudanar da bukin radin sunan, ya kuma zanta da ita, inda ta bayyana cewa wannan ne karo na ukku da ta shirya irin wannan taro.

"Ba wannan bane karo na farko, sau ukku ke nan uwar garken tana haihuwa, kuma duk haihuwa sai na yi bukin radin sunan awakin da ta haifa. A wajena, wannan ba bakon abu bane," a cewar Hajiya Fatima.

Ba wai taron bukin radin sunan kadai ya dau hankali jama'a ba, a'a, yadda akaga Hajiya Fatima tare da cincirindon kawayenta sun sanya kaya iri daya, da sunan Ashobe (Anko).

"Kamar yadda ake yin Ashobe (anko) a wajen bukukuwa, haka nima naga ya dace na rabawa kawayena ashoben radin sunan awakina," a cewar ta.

DUBA NAN: Kaico! Wata mahafiya ta kashe ‘ya’yanta mata guda 2 a jahar Imo

Dangane da sunan da ta sanyawa awakan kuwa, Hajiya Fatima ta ce: "Ba laifi bane a wajena don na sanyawa awakaina sunan Afra da Afnan, domin har a raina ina sonsu, kuma ko da ace 'yayan da zan haifa ne zan iya sanya masu wadannan sunaye."

"Tun da nake kiwo, ban taba cin karo da uwar garke mai albarka kamar uwarsu Afra da Afnan ba, domin tana haihuwa akai akai, 'yan biyu na biyu kenan yanzu. Kunga kuwa dole na rinka yin bukin radin sunan su."

Dama dai Hausawa sun yi magana, sunce abincin wani, gubar wani. A yayin da Hajiya Fatima ta yi wannan bukin radin suna, a hannu daya kuwa, da yawa na ganin cewa hakan kawai wata sabuwar al'ada ce ta dauko wacce babu ita a al'adar Malam Bahaushe.

Kalli hotunan bikin:

Ana ga wata, ga wata: An yi bukin radin sunan awakai biyu, Afnan da Hanifa
Awakan
Source: Facebook

Ana ga wata, ga wata: An yi bukin radin sunan awakai biyu, Afnan da Hanifa
Matan
Source: Facebook

Ana ga wata, ga wata: An yi bukin radin sunan awakai biyu, Afnan da Hanifa
Mai awakan
Source: Original

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel