Yansanda sun kama Magidanci da laifin kashe makwabcinsa a kan ‘musu’

Yansanda sun kama Magidanci da laifin kashe makwabcinsa a kan ‘musu’

Rundunar Yansandan jahar Legas ta sanar da kama Segun Mopoderun da laifin kashe makwabcinsa bayan kaurewar wata zazzafar musu a tsakaninsu, kamar yadda rahoton jaridar Sahara Reporters ta bayyana.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Segun mazaunin layin Ogba-Aguda ne dake cikin unguwar Agege ta jahar Legas, ana zarginsa da laifin antaya ma makwabcinsa ruwan zafi mai suna Oposanwo Gbenga dan shekara 58, wanda ya yi sanadiyyar mutuwarsa.

KU KARANTA: Wasu Malamai 2 sun yi ta maza, sun arce daga hannun barayin mutane da suka yi garkuwa dasu

Kaakakin Yansandan jahar, Bala Elkana ya bayyana cewa koda yake mamacin bai mutu a inda aka watsa masa ruwan zafin nan take ba, amma ya mutu ne a yayin da ak garzaya da shi zuwa wani babban asibiti.

“Da misalin karfe 6:30 na safiyar Asabar, 16 ga watan Nuwamba wani mutumi mai suna Segun Mopoderun dake gida mai lamba 3, Ogba-Aguda ya watsa ma wani mutumi, Oposanwo Gbenga mai shekaru 58 ruwan zafi biyo bayan sabani da suka samu.

“Ba tare da wata wata ba aka garzaya da mamacin zuwa asibiti domin samun kulawa, inda ya mutu a can. An jibge gawarsa a dakin ajiyan gawa na babban asibitin Ikorodu domin a gudanar da bincike.” Inji shi.

Daga karshe kaakaki Elkana ya tabbatar da kama wanda ya aikata laifin, sa’annan yace sashin binciken manyan laifuka na jahar sun fara gudanar da bincike a kan lamarin.

Wasu malaman makarantun gaba da sakandari guda biyu yan gida daya da wasu miyagu yan bindiga suka yi garkuwa dasu sun tsallake rijiya da baya sun tsere daga hannun barayin mutanen bayan an biya kudin fansa naira miliyan 5.

Malaman sun hada da Adamu Chonoko dake koyarwa a jami’ar Ahmadu Bello da Umar Chonoko dake koyarwa a kwalejin kimiyya da fasaha na gwamnatin tarayya dake garin Kaduna, sun tsere ne bayan kwashe kwanaki 10 a hannun miyagun

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel