An kama tsohon ministan shari'ar Najeriya a kasar Dubai

An kama tsohon ministan shari'ar Najeriya a kasar Dubai

Jaridar Premium Time ta gano cewa, hukumar 'yan sandan kasa da kasa sun cafke Muhammad Bello Adoke, tsohon ministan shari'ar Najeriya a Dubai.

Mutanen da suka gano wannan cigaban sun ce, an kama Adoke ne jim kadan bayan ya isa Dubai a ranar 11 ga watan Nuwamba. Ya je kasar ne don duba lafiyarsa bayan kotu ta janye bukatar kamasa a watan Oktoba.

Jastis D. Z Zenchi na babbar kotun tarayya ne ya bada umarnin kama tsohon ministan shari'ar bayan bukatar da hukumar yaki da rashawa ta mika gaban kotun.

EFCC ta dade tana bibiyar Adoke bayan ikirarin yana da hannu a kwangilar man fetur ta Malabu. Adoke ya musanta hannunsa a cikin wannan damfarar da ake zarginsa da ita kuma ya tsere da kansa tun a watan Mayu na 2015.

Ya dade yana dogaro da hukuncin kotu da tace, ba za a iya gurfanar dashi ba a kan aikin da yayi yana ofishinsa kuma karkashin umarnin fadar shugaban kasa.

Jastis Zenchi ya soke umarnin kama shi ne a ranar 25 ga watan Oktoba bayan rokon da lauyan Adoke ya yi.

Alkalin ya kara da umartar hukumar yaki da rashawa da ke son gurfanar da Adoke da su yi amfani da wata hanya don mika masa takardun kotun.

DUBA WANNAN: Kogi: Musa Wada ya ce bai aminta da sakamakon zabe ba

Akwai yuwuwar hukumomi daga Najerriya basu sanar da 'yan sandan kasa da kasa cigaban ba.

An gano cewa, 'yan sandan sun yi mamaki da Adoke ya sanar dasu cewa, an soke umarnin kamashi din a don haka babu dalilin yin hakan.

Majiya tace, a halin yanzu, hukumomin 'yan sandan kasa da kasan sun bukaci hukumomin da abun ya shafa a Najeriya da su sanar dasu cigaban da aka samu a kan hakan.

Ma'aikatar shari'a a Abuja na ta kokarin turawa 'yan sandan kasa da kasar a Dubai matsaya a kan umarnin don samun su saki Adoke amma hakan ta ci tura saboda shugaban ma'aikatar shari'a, Abubakar Malami baya nan, in ji wata majiya.

Har zuwa ranar Lahadi ba a samu Malami ba don tsokaci a kan lamari. Hakazalika, mai magana da yawun 'yan sandan kasa da kasar ya ce ba zai iya magana a kan Adoke ba saboda ya shafi UAE ne.

Ba a dade da sa hannu a wata yarjejeniya tsakanin Najeriya da UAE ba. Duk wanda a ke zargi da rashawa daga Najeriya za a iya cafkesa a UAE din kuma a dawo da shi Najeriya don fuskantar hukunci. Kuma za a iya kwace kadarorinsa a da ke kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel