Yanzu-yanzu: An sace ma'aikacin INEC a Lokoja

Yanzu-yanzu: An sace ma'aikacin INEC a Lokoja

An sace wani ma'aikacin Hukumar zabe mai zaman kanta na kasa (INEC) a rumfar zaben SUBEB dake Lokoja a jihar Kogi.

An sace shi bayan wasu 'yan daba dauke da bindigu sun afkawa masu zabe suna harbe-harbe a iska yayin da ake gudanar da zaben.

The Nation ta ruwaito cewa masu zaben sun cika wandunansu da iska tun kafin 'yan bindigan suyi awon gaba da ma'aikacin na INEC.

Sai dai tuni an kammala kada kuri'u a rumfar zabe dake makarantar frimare ta Bishop Crowther dake lokoja.

DUBA WANNAN: Tirkashi: An kamo Dino Melaye yana siyan kuri'u (Hoto)

Za a fara tantance kuri'un da kuma kidaya misalin karfe 2 na rana.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel