Bidiyo: Wani dalibin karshe a jami'ar Najeriya ya kera jirgin sama ya gwada shi yayi aiki

Bidiyo: Wani dalibin karshe a jami'ar Najeriya ya kera jirgin sama ya gwada shi yayi aiki

- Wani dalibin shekarar karshe a jami’ar Najeriya ya samu lambar yabo bayan da ya kammala hada jirgin sama

- Dalibin shekarar karshen, ya kammala hada jirgin ne a matsayin aikinsa na cike digirinsa kuma ya gwadashi cikin nasara

- A wani bidiyo da ake gwajin jirgin dalibin ya samu jinjina daga ‘yan uwanshi dalibai bayan da jirgin ya lula sararin samaniya

Wani dalibin shekarar karshe a jami’ar fasaha ta gwamnatin tarayya da ke Owerri ya zama abin kwatance da alfahari ga ‘yan Najeriya. Ya yi nasarar hada jirgin sama wanda ya tashi a matsayin aikinsa na shekarar karshe a jami’ar.

Injiniyan da har yanzu ba a san sunanshi ba, ya hada jirgin a shekarar shi ta karshe a jami’ar. Karin farin cikin dalibai da yawa, jirgin saman ya tashi inda ya lula a sararin samaniya kamar dai yadda jirgin sama ke yi.

A wani bidiyo da wani shafi na Twitter mai suna SubDeliveryZone ya wallafa, an ga dalibin ya tashi jirgin saman yayin da dalibai ‘yan uwanshi suka taru don shaida wannan nasarar. Bayan wani lokaci, an ga jirgin saman ya fara tafiya kafin daga baya ya daga kacokan zuwa sararin samaniya.

KU KARANTA: Allahu Akbar: Wata mata ta shafe shekara 32 tana saka Al-Qur'ani mai girma da zare da allura tun daga Bakara har Nasi

Ba wannan ne karo na farko da aka fara samun matasa masu hazakar kirkire-kirkire a kasar nan ba. Babbar matsalar itace, ba a basu damar baje kolin hazaka da fasahar da Allah ya yi musu.

Da yawa daga cikin mutane masu wannan fasahar ta kirkire-kirkire kan yi abubuwan ban mamaki matukar suka samu damar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel