Miyagun makiyaya sun halaka mutane guda 4 a jahar Kaduna

Miyagun makiyaya sun halaka mutane guda 4 a jahar Kaduna

Rundunar Yansandan jahar Kaduna ta sanar mutuwar wasu mutane hudu a hannun wasu gungun Fulani makiyaya yan bindiga a unguwar Marban Agban dake cikin masarautar Kagoro cikin karamar hukumar Kauran jahar Kaduna.

Rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya ta bayyana kaakakin rundunar Yansandan jahar, DSP Yakubu Sabo ne ya tabbatar da haka yayin da yake ganawa da manema labaru a Kaduna a ranar Juma’a.

KU KARANTA: Dan daba ya shiga har cikin makaranta ya kashe wani dalibi a gaban Malamansa a Kaduna

Kaakakin ya bayyana sunayen wadanda aka kashe a sakamakon harin kamar haka; Hosea Ayuba, Ada Adamu, Abagu Danladi da Kusa Danladi, dukkaninsu a unguwar Marabar Agban, sa’annan makiyayan suka yi awon gaba da dabbobinsu guda uku.

“Da misalin karfe 3 na rana aka samu rahoton bullar barayin shanu tare da kisan wanda aka sanar da jami’an Yansandanmu dake garin Kafanchan yayin da suke aikin binciken a wani shingen ababen hawa.” Inji shi.

Kaakakin yace ba tare da wata wata ba Yansanda a karkashin jagorancin kwamandan ofishin Yansandan suka bazama aiki, inda suka kama wata motar Bus mai lamba BLD 43 XA dauke da wasu shanu guda 3 da suke zargin na sata ne.

Daga nan Yansandan suka kama diraben motar mai suna Sadiq Umar da kuma Umar Abubakar, dukkaninsu mazauna Unguwar Nungu cikin karamar hukumar Jama’a, haka zalika Yansanda sun kama wani babur mai lamba QC 717 AKW mallakin guda daga cikin maharan.

Daga karshe kaakakin Yansandan ya yi kira ga jama’a dasu basu hadin kai tare da goyon baya a kokarin da suke yin a magance matsalar tsaro da sauran miyagun laifuka a yankin da ma jahar gaba daya.

A wani labarin kuma, rundunar Yansandan jahar Kaduna ta tabbatar da kama wani gagararren dan daba mai suna Sani Umar sakamakon tuhumarsa da ake yi da laifin kisan kai bayan ya kashe wani dalibin makarantar sakandari mai suna Hassan Abdullah.

Sani Umar ya kashe Hassan ne a ranar Alhamis, 14 ga watan Nuwamba a lokacin da ya shiga har cikin makarantar sakandari ta Rigachikun dake cikin karamar hukumar Igabi, inda ya soka masa wuka a gaban malamansa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel