To fah: Fasto ya ciyar da mabiyanshi masu neman karama da tsutsotsi a cikin coci

To fah: Fasto ya ciyar da mabiyanshi masu neman karama da tsutsotsi a cikin coci

- Wani fasto a kasar Afirka ta kudu mai suna Lesego Daniel, ya ciyar da mabiyansa da matsatsaku da giya

- Faston ya wallafa hotunan yadda abun ya faru ne a shafinsa na yanar gizo

- A cewarsa, komai da aka halitta a duniya abinci ne, dan adam zai iya cinsa kamar yadda aka halitta tsirrai don shi

Wani fasto a kasar Afirka ta kudu mai suna Lesego Daniel, ya yada hotunan yadda ya ciyar da mambobin majami'arsa da matsatsaku da giya.

A rubutun da ya wallafa a shafinsa na yanar gizo, ya bayyana cewa, duk abinda ubangiji ya halitta a duniya, dan adam zai iya ci.

Ga abinda Faston ya rubuta kamar haka: "A cocin mu ta Rabboni, fastonmu ya tabbatar da cewa, duk abinda ubangiji ya halitta, dan adam zai iya ci. Saboda haka ba zamu nuna banbanci ba, saboda duk abinda ke rayuwa kuma yake motsi a duniya tabbas zai iya zama abinci, kamar yadda ya bamu tsirrai a matsayin abinci."

"Ya sanar da Nuhu a Genesis ta 9, cewa na baka komai a matsayin abinci. Don haka a yau muke bayyana wadanda ke tafarkin ubangiji."

KU KARANTA: Tirkashi: Mai gari yayi walankeluwa ya fada cikin kabari ya ce allan fur baza a binne wasu ma'aurata ba

"Haka ne yasa 'ya'yan albarka ba a yanke musu hukunci da abinda suka ci ko suka sha ko kuma abinda ya danganci bukukuwan addini. Saboda haka ba zamu jira ba, ko menene muka samu zamu ci daga kan kaza, matsatsaku, tana da sauransu. Zamu ci mu sha da kalmomin ubangiji tare da addu'a."

"Ta haka ne muke kiran ubangiji Yesu, da duk 'ya'yansa maza da mata da suka fito daga jikinsa cikin jindadi. Babu shakka zasu ga haske da kalaman gaskiya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel