An gano kauyuka 67 a Abuja da ake kashe tagwaye da zabiya da zarar an haife su

An gano kauyuka 67 a Abuja da ake kashe tagwaye da zabiya da zarar an haife su

- Garuruwa 67 ne aka bankado a yankuna 5 na birnin tarayyar Abuja da ke kashe tagwaye

- Ba a kan tagwaye kadai lamarin tsaya ba, hatta jaririn da aka haifa 'yan uku, zabiya, jariran da mahaifiyarsu ta rasu wajen haihuwa duka suna kashewa

- Duk da rahoton bai bayyana dalilinsu na yin haka ba, babu shakka za a iya samu lamarin camfi tattare da hakan

Garuruwa 67 ne a yankuna 5 na birnin tarayyar Abuja ke da hannu dumu-dumu a kashe tagwayen, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Owanbi da Chakumi a yankin Gwagwalada; Makana da Dudu a cikin birnin Abuja; Gulida da Zuhi a yankin Abaji; Kehi a yankin Kuje, sune kadan daga cikin mutanen da suke aikata wannan muguwar ta'asa.

Kamar yadda rahotanni suka nuna, a wadannan yankunan, ana halaka yara tagwaye, 'yan uku, zabiya, nakasassu, wadanda hakoran gaba suka fara fitowa da kuma yaran da mahaifiyarsu ta rasu yayin haihuwarsu.

Wannan mummunan lamarin na faruwa ne a wasu a cikin wasu kauyuka na babban birnin tarayyar Abuja dake Najeriya.

KU KARANTA: Bincike: An gano cewa gajerun mutane sun fi dogayen mutane shiga damuwa a duniya

A tarihin lokacin jahilliyyah kafin zuwan Annabi Muhammadu SAW ake binne 'ya'ya mata da ransu, sai dai zuwan addinin Islama ke da wuya kuwa aka haramtawa larabawa aikata wannan rashin imanin.

A tarihin Najeriya akwai zamanin da tarihi ya nuna ana kashe tagwaye, lokacin zuwan turawan mulkin mallaka kuwa ya wayar da kan mutane aka daina aikata wannan rashin imanin.

Amma kwatsam sai gashi an binciko tare da bankado wasu al'umma da suke aikata wannan rashin tausayin.

Duk da dai ba a san dalilinsu na yin haka ba, amma babu shakka idan aka bincika za a gano abin yana da nasaba da camfi. Don shi ne sillar yawancin wadannan rashin tausayin ga rayukan bil adama.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng