Kasar Nijar ta bayyana irin asarar da ta tafka sakamakon rufe iyakokin Najeriya

Kasar Nijar ta bayyana irin asarar da ta tafka sakamakon rufe iyakokin Najeriya

Kasar Nijar, mai makwabataka da Najeriya ta bangaren arewa, ta bayyana cewa rufe iyakokin Najeriya na kasa ya jawo mata asarar makudan kudin da yawansu ya kai kudin kasar CFA Miliyan 40, kimanin dalar Amurka miliyan $67, kwatankwacin fiye da biliyan N24 a kudin Najeriya.

Nijar ta bayyana hakan ne ta bakin Diop Mamadou, ministan kudin kasar, yayin halartar wani taro na wakilan kasashen da rufe iyakokin Najeriya na kasa ya shafa da ake yi a Abuja.

Wakilan gwamnatocin kasashen Benin, Najeriya da kuma Nijar sun fara wani taro a Abuja domin tattauna wa tare da yin duba a kan halin da kasashen suka tsinci kansu tun bayan rufe iyakokin Najeriya na kasa.

Ministan kudin kasar Diop Mamadou ya ce ya kamata a ce wannan kudi sun shiga baitulmalin kasar.

Mamadou ya bayyana cewa kamata ya yi a ce adadin makudan kudin da ya ambata sun shiga asusun kasar Nijar, amma hakan bata samu yiwu ba sakamakon rufe iyakokin da Najeriya ta yi tun a cikin watan Agusta.

DUBA WANNAN: Dalilin sauke mataimakin kakakin majalisar jihar Gombe

Wasu 'an kasuwa a kasar Nijar sun bayyana cewa su ma sun tafka asara mai yawan gaske, wasu daga cikinsu ma sun ce karyewa suka yi gaba daya a saboda rufe iyakokin.

Alhaji Mati Yamai, wani dan kasuwa a kasar Nijar, ya ce kamata ya yi a nemi hanyar warware matsalar rufe iyakokin Najeriya saboda asarar da suke tafka a harkokin kasuwancinsu na yau da kullum.

Dan kasuwar ya shaida wa BBC Hausa cewa tilas ya sa aka mayar da kayansa Kano sakamakon makalewar da suka yi a bakin iyakar Najeriya da Nijar.

Kusancin da ke tsakanin Najeriya da kasar Nijar ya sa ana samun kulla harkallar kasuwanci da kuma zirga-zirgar jama'a a tsakanin kasashen biyu a kowacce rana.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel