Ba zaka taba zama shugaban kasa ba - Anglican Bishop ga El-Rufa'i

Ba zaka taba zama shugaban kasa ba - Anglican Bishop ga El-Rufa'i

Shugaban cocin Anglica na Zariya, Rt Rev Abiodun Ogunyemi, ya ce gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ba zai taba zama shugaban kasan Najeriya ba saboda da alamun abinda yake shirin yi kenan a 2023.

Faston ya bayyana hakan ne kan kokarin rusa wani dukiyan Cocin bayan an yi kokarin rusa coci mai tarihin shekaru 110 na George Cathedral, Sabon-Gari Zaria.

Fasto Ogunyemi, ya caccaki takwararsa na garin Wusasa, Rev. Ali Buba Lamido, wanda ya yabawa gwamna El-Rufa'i kan tsagaita rusa cocin ranar Litinin.

Fasto Ogunyemi ya gargadi El-Rufa'i kan kokarin fusata cocin a Kaduna saboda hakan fito-na-fito da Allah ne kuma da Kiristoci a fadin tarayya.

Faston ya ce cocin ba yaki take da gwamnan ba, kawai tana yakin kare hakkinta ne kuma babu wanda zai iya hanasu kwato hakkinsu.

Yace: "Duk wani yunkurin rusa dukiyoyinmu a kasuwa fito-na-fito ne da dukkan Cocina a Najeriya."

"Ana shiryashi domin takara a 2023. Gwamnan ya sani cewa ba zai taba zama shugaban kasa Najeriya ba."

DUBA NAN Yanzu-yanzu: Gwamna Masari ya sake maka Lado da kasa a kotu

Kotun daukaka kara reshen Kaduna a ranar Alhamis, 7 ga watan Nuwamba, ta tabbatar da zaben Malam Nasir Ahmad El-Rufai, a matsayin gwamnan jihar Kaduna a zaben gwamna da aka yi a ranar 9 ga watan Maris, 2019.

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da dan takararta, Isah Ashiru ne suka daukaka kara a gaban kotun, inda suke kalubalantar hukuncin kotun zabe, wacce ta kaddamar da El-Rufai a matsayin wanda ya lashe zaben.

Hukumar zabe mai zaman kanta da fari ta kaddamar da El-Rufai a matsayin wanda ya lashe zaben.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel