Yanzu-yanzu: Gwamna Masari ya sake maka Lado da kasa a kotu

Yanzu-yanzu: Gwamna Masari ya sake maka Lado da kasa a kotu

Kotun daukaka kara dake zamanta a Kaduna ta yi watsi da karar da Sanata Yakubu Lado da jam'iyyar PDP suka shigar kan gwamnan jihar Katsina, Aminu Belli Masari, jam'iyyar APC da hukumar INEC.

Alkalan kotun daukaka karan sun yi ittifaki wajen yanke wannan hukunci kuma sun tabbatar da nasarar Aminu Masari a zaben watan Maris, 2019.

Za ku tuna cewa a watan Satumba, kotun zaben jihar Katsina ta tabbatar da Aminu Bello Masari matsayin zakaran zaben 2019.

Sakamakon haka, Sanata Lado Yakubu da jam'iyyarsa ta PDP suka garzaya kotun daukaka kara domin kalubalantar hukuncin.

A wani labarin daban, Kotun daukaka karar dake zamanta a Makurdi, jihar Benue ta tabbatar da Injiniya Abdullahi Sule na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) matsayin zababben gwamnan jihar Nasarawa a ranar Talata, 12 ga Nuwamba, 2019.

Kotun ta yi watsi da karar da jam'iyyar People Democratic Party (PDP) da dan takararta, Emmanuel David Ombugadu, suka shigar kan zaben 9 ga Maris.

Kotu ta kara da cewa ko shakka babu ta amince da hukuncin kotun zabe da ta yanke cewa lallai Abdullahi Sulene ya lashe zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel