Gwamna Fintiri zai biya ma’aikata a Adamawa karancin albashin N32,000

Gwamna Fintiri zai biya ma’aikata a Adamawa karancin albashin N32,000

Gwamnan jahar Adamawa, Ahmadu Fintiri zai fara biyan ma’aikatan gwamnati karancin albashin N32,000, fiye da N30,000 da gwamnatin tarayya ta amince, daga karshen watan Nuwamba da muke ciki.

Rahoton jaridar Daily Trust ta ruwaito shugaban ma’aikatan jahar, Dakta Edgar Amos ne ya bayyana haka a ranar Laraba, 13 ga watan Nuwamba, inda yace gwamnatin jahar za ta fara biyan wannan kudi daga Nuwamba domin cika alkawarin da Gwamna Fintiri ya dauka na biyan ma’aikata N32,000.

KU KARANTA: Gwamnan Borno ya sanya ma makafi, kurame da guragu 3,127 albashin dubu Talatin-talatin

“Sabon karancin albashi a Najeriya N30,000 ne, toh amma gwamna zai biya N32,000 ne saboda shi ne alkawarin daya daukan a yayin yakin neman zabensa.” Inji shugaban ma’aikatan jahar Adamawa.

Sai dai Dakta Edgar yace har yanzu gwamnati na tattaunawa da kungiyoyin kwadago kan yadda za’a daidaita dokar sabon karancin albashin ga ma’aikatan da suke amsan albashin daya haura karancin albashi.

Idan za’a tuna, gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ne ya fara biyan ma’aikata sabon karancin albashi a Najeriya, inda malaman makarantun firamari da sakandari dake amsan albashin N30,000 zuwa N33,000 suka samu karin N20,000 a albashinsu.

A wani labarin kuma, Gwamnan jahar Borno, Babagana Umara Zulum ya kirkiro da tsarin tallafa ma mutane masu nakasa dake yawon barace barace a jahar, inda ya sanya musu albashin N30,000 a kowanne wata.

Kwamishinan yaki da talauci na jahar Borno, Nuhu Clark ne yace tsarin ya kunshi mabarata da suka hada da kurame, makafi da kuma guragu da yawansu ya kai 3,127 daga cikin mutane 7,000 a duk fadin jahar dake cikin gajiyar wannan tsari na albashin N30,000.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel