Tashin hankali: Birai sun afka wani kauye suna duka da kashe mutane haka siddan

Tashin hankali: Birai sun afka wani kauye suna duka da kashe mutane haka siddan

- Na daga cikin kalubalen da kasar Uganda ke fuskanta, shine harin da birai suke kai wa mutane

- Abun ya fara ne a shekarar 2014, yayin da biri ya kashe yaro ta hanyar balla masa kafada, raunata masa kai da kwakule masa koda

- Wata mata mai 'ya'ya hudu ta bayyana yadda suka yi gudun hijira suka bar gidajen su saboda birirrukan

Wani rahoto da tashar National Geography ta fitar ta ce, matsalolin kai hare-hare da birai suke yi akan mutane a kasar Uganda sun fara ne tun shekarun baya. A shekarar 2014 wani biri ya sace yaro daga wajen mahaifiyarsa.

"Birin ya shigo lambun mu lokacin ina haka rami," Ntegeka Semata ta sanar a wata tattaunawa da aka yi da ita.

Ta bayyana cewa, yaranta hudu kanana na tare da ita, ta juya don diban ruwa kwatsam birin ya kwace danta kuma ya ranta a na kare.

Yaron yayi ihu, abinda ya jawo hankulan 'yan kauyen kuma suka bi shi. Amma kash, sun yi latti domin kuwa, "birin ya karya masa kafada, ya fasa masa kai da cikinsa inda ya cire masa koda," Semata ta kara da bayyana yanda dan ta ya rasu a hanyarsu ta zuwa asibiti.

Semata da mai gidanta suna rayuwa ne a kauyen fiye da shekaru uku. Sun yi katangar da ta zagaye gidansu don ta zama kariya daga biran. "Ina tsoro idan na tuna cewa wasu biran zasu iya zuwa," Semata ta ce a hirar da aka yi da ita.

KU KARANTA: Tashin hankali: Saurayi ya kashe dan uwanshi na jini saboda ya zagi budurwarshi

Biran sun cigaba da zuwa duk kuwa da katangar, lamarin da yasa Semata da mijinta suka bar gidan a karshen shekarar 2017, suka koma wani gidan baya.

Tun bayan aukuwar lamarin a 2014, an cigaba da samun hare-haren biran a Muhororo ga yara. An ruwaito cewa yara uku sun mutu tare da raunata guda shida duka sakamakon hare-haren.

Babu bayyanannen dalilin da yasa biran suke kai harin ga kananan yara amma ana zargin rashin mafakarsu ne a yammacin kasar.

"Dajin da ke rufe da tsaunikan a da, yanzu duk babu shi. An rika sarar itace da bishiyoyi tare da samun filin shuka," in ji rahoton da National Geography ta fitar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel