Dandalin Kannywood: Maryam Yahaya ta karkata daga harkar Fim zuwa sabuwar sana’a

Dandalin Kannywood: Maryam Yahaya ta karkata daga harkar Fim zuwa sabuwar sana’a

Shahararriyar tauraruwar fina finan Kannywood, Maryam Yahaya ta fadada hanyoyin samun kudinta, inda ta karkata daga harkar fitowa a fina finai kadai don samun kudi zuwa wata sabuwar sana’a ta daban.

Maryam ta bude wani katafaren shagon yi ma mata kwalliya da wankin gashi ne a cikin birnin Kano, wanda ta sanya masa sunanta, kamar yadda ta bayyana a shafinta na kafar sadarwar zamani na Instagram @real_maryamyahaya.

KU KARANTA: Yan bindiga sun kashe magajin garin wani kauye, sun sanya ma jama’a haraji

An hangi yan uwa da abokan arzikin Maryam a wajen bikin kaddamar da katafaren shagon, fitattu daga cikin wadanda aka hanga a wajen har da jarumi Sarki Ali Nuhu.

Ita dai Maryam ta fara samun shahara ne a cikin wani Fim mai suna ‘Mansoor’ da aka shirya shi a shekarar 2016, daga nan kuma ta fito a wani Fim mai suna ‘Hafeez’, ‘Sareena’ ‘Tabo’ da dai sauransu.

Idan za’a tuna a kwanakin baya ne shahararriyar jarumar fina-finan hausa, Maryam Yahaya ta bayyana dalilin da ya hanata aure. Jarumar ta bayyana hakan ne a hirar da tayi da gidan rediyo na Freedom dake Kano.

Jarumar tace: "Da aure da mutuwa duk lokaci ne, idan lokaci kuwa yayi ai zan daga. Baabu mijin ne, hakan ne ya hanani auren. Ku fito ku aureni, kunsan aure maza yanzu wuya suke."

A kwankin baya ne dai hotuna suka dinga yawo a kafafen sada zumunta ana cewa, an kasa Maryam Yahaya don kuwa saurayinta Maishadda zai angwance da matashiyar jaruma Hassana Muhammad.

Sai dai, a wata hirar da gidan rediyon Freedom yayi da Abubakar Bashir Maishadda, ya tabbatarwa da gidan rediyon cewa tabbas ya taba soyayya da Maryam amma Allah ne bai nufa zai aureta ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel