Wani mutum ya sari kaninsa da adda kan zargin yana kwartanci da matansa (Hoto)

Wani mutum ya sari kaninsa da adda kan zargin yana kwartanci da matansa (Hoto)

- Wani magidanci ya yi sanadiyar kwanciyar kaninsa jinya a gadon asibiti a birnin tarayya Abuja

- Magidancin ya yi zargin kaninsa na soyayya da matarsa ne hakan ya sa ya yi masa rauni da adda

- Lamarin ya faru ne a unguwar Abaji dake babban birnin tarayya Abuja kamar yadda wani Abdulkareem Lukman ya bayyana a Facebook

Wani mutum yana kwance rai a hannun Allah bayan an ce yayansa ne ya sare shi da adda kan zarginsa da yin soyaya da matarsa.

Kamar yadda wani ma'abocin amfani da shafin sada zumunta na Facebook, Abdulkareem Lukman ya bayyana, lamarin ya faru ne a garin Abaji dake babban birnin tarayya Abuja.

Ga dai abinda ya rubuta a shafinsa na Facebook din a ranar Talata: "Ban san inda duniya za ta kai mu ba. Ta yaya mutum mai cikakken hankali da tunani zai yi amfani da adda ya yi wa kaninsa rauni... Mataashin dake kwance a asibiti ya tsinci kansa a halin ne saboda yayansa. Yayan ya yi ikirarin cewa kaninsa yana soyayya da matarsa kuma ba tare da yin wani bincike ba bayan ya dawo daga gona sai ya raunata kaninsa. Don Allah kuyi masa addu'an samun sauki cikin gaggawa."

DUBA WANNAN: 'APC' ta dakatar da wani gwamna da mataimakinsa akan zargin zasu koma PDP

Wani mutum ya sari kaninsa da adda kan zargin yana kwartanci da matansa
Wani mutum ya sari kaninsa da adda kan zargin yana kwartanci da matansa
Asali: Twitter

Mutane da dama sun bayyana ra'ayoyinsu kan lamarin. Yayin da wasu ke ganin yayan ya yi saurin yanke hukuncin tunda bai gudanar da bincike ya tabbatar da zargin ba wasu kuma na ganin kanin nasa ya yi cin amana amma dai bai kamata mutum ya dauki doka a hannunsa ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel