Yanzun nan: Gobara ta tashi a fadar gwamnatin jahar Neja dake Minna

Yanzun nan: Gobara ta tashi a fadar gwamnatin jahar Neja dake Minna

Wata gobara ta tashi a fadar gwamnatin jahar Neja dake garin Minna, babban birnin jahar, inda ta tafka mummunan barna, kamar yadda rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta bayyana.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wutar ta taso ne daga ofishin babban sakataren fadar gwamnatin sakamakon matsala da aka samu daga wayoyin wutar lantarki dake cikin ofishin, sai dai babu motar kashe gobara a fadar gwamnatin.

KU KARANTA: An ci moriyar ganga: Matashi ya hana wata kilaki kudinta, sa’annan ya kasheta

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 12:30 na ranar Talata, sai dai ba tare da bata lokaci ba jami’an hukumar kashe gobara suka isa fadar gwamnatin daga ofishinsu na jahar Neja, inda suka samu nasarar kashe wutar bayan mintuna 15.

Majiyarmu ta bayyana cewa an hangi ma’aikatan fadar gwamnatin suna gudun tsira, watau idan baka yi bani wuri, kafin isowar jami’an hukumar kwana kwanan, wanda suka isa gidan gwamnatin da manyan motoci guda uku makare da ruwan kashe gobara.

Sai dai wannan wutar ta tafka mummunan barna a ofishin babban sakataren, inda ta lakume muhimman takardu da kuma kayan aiki a ofishin da suka hada da kujeru, wayoyin salula na kan teburi, kwamfutoci da tebura.

Mataimakin shugaban hukumar kashe gobara na jahar Neja, Malam Salihu Bello ya bayyana cewa isowarsu fadar gwamnatin cikin gaggawa ya taimaka wajen takaita barnar da gobarar ta tafka a ofishin.

Sai dai Bello yace rashin motar kashe gobara a fadar gwamnatin jahar ba da gangan bane, kuma ba wai sakaci bane, inda yace akwai shirin da gwamnatin jahar ke yi na samar da motocin kashe gobara a fadar gwamnatin.

Ita ma a nata jawabin, Mary Berje, babbar sakatariyar gwamnan jahar Bello, Gwamna Sani Bello ta bayyana cewa akwai motocin kashe gobara a fadar gwamhatin, amma an kaisu gyara ne.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel