Ministocin Buhari 22 da babu su a shafin yanar gizo na gwamnatin tarayya

Ministocin Buhari 22 da babu su a shafin yanar gizo na gwamnatin tarayya

Sama da watanni biyu bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da ministocinsa, sunayen ministoci 22 cikin 43 da aka rantsar basa shafin yanar gizo na gwamnatin tarayyar.

A ranar 21 ga watan Augusta ne shugaban kasan ya rantsar da sabbin ministocinsa a fadar shugaban kasa sannan ya basu ma'aikatun da zasu jagoranta.

Amma kuma da aka duba shafin yanar gizon gwamnatin tarayyar a ranar Litinin ya nuna ma'aikatu 37 ne shafin a maimakon 43. Sauran da babu su ne sabbin ma'aikatun da Buhari ya kirkira ko kuma ya fitar daga cikin wasu tsoffin ma'aikatun, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

A cikin 37 din, 21 ne kadai aka wallafa sunayen ministocin da ke jagorantar ma'aikatun. Sauran gurabe 16 babu sunayen ma'aikatun ko kuma babu sunan ministan da ke jagorantar ma'aikatar.

Ma'aikatun da a ka lissafo a shafin babu sunan ministan sune: Ma'aikatun masana'anta, kasuwanci da hannayen jari, harkokin Neja Delta, karamin ministan Neja Delta, man fetur, karamin minisatn man fetur, wutar lantarki, gidaje da aiyuka, karamin ministan wutar lantarki, aiyuka da gidaje, kimiyya da fasaha, albarkatun kasa da karamin ministan albarkatun kasa.

Sauran ma'aikatun sun hada da ma'aikatar sufuri, ma'aikatar harkokin sufurin jiragen sama, ma'aikatar ruwa, ma'aikatar harkokin mata da kuma ma'aikatar matasa da wasanni.

Duk da tuni aka maida Festus Keyamo ma'aikatar Tayo Alasodaura inda shima Tayo ya koma ma'aikatar Keyamo, a jerin sunayen sun bayyana ne a tsoffin ma'aikatunsu.

DUBA WANNAN: An kai hari gidan casun Saudiyya

Zainab Ahmed kuwa ta bayyana ne a matsayin ministar kudi, tsohon sunan ma'aikatarta. Mustapha Shehuri kuwa ya bayyana ne a ma'aikatar noma da habaka karkara.

Sabbin ma'aikatun da aka kirkiro kuwa basa cikin jerin.

Ministocin da kwata-kwata babu sunansu kuwa a jerin sun hada da: Rotimi Amaechi, Gbemisola Saraki, Hadi Sirika, Sulieiman Adamu, Pauline Tallen, Sunday Dare, Mohammed Nanono da Niyi Adebayo.

Sauran sun hada da Maryam Katagum, Godswill Akpabio, Mimipre Sylva, Babatunde Fashola, Ogbonnaya Onu, George Akume, Mohammed Dangyadi, Mohammed Abdullahi, Sharon Ikeazor, Olamilekan Adegbite, Abubakar Aliyu, Sadiya Faruk, Godwin Jedi-Agba da Ramatu Aliyu.

Mai magana da yawun kungiyar yarbawa ta Afenifere, Yinka Odumakin, ta kwatanta wannan cigaba da gazawar gwamnatin. Hakan kuwa kungiyar ta kwatanta da abinda ke kawo gazawa a mulkin gwamnatin nan.

Odumakin yace, " A ce sunayen ministoci 22 babu su a shafin gwamnatin tarayya tun bayan watanni biyu da rantsar da ministocin na bayyana gazawar wannan gwamnatin ne. Maganar gaskiya, ba a maida hankali akan wadannan kananan abubuwan da ke da amfani."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel