Assha: Jami'an 'yan sanda sun cafke barayi wajen Maulidi

Assha: Jami'an 'yan sanda sun cafke barayi wajen Maulidi

A ranar Litinin ne hukumar 'yan sandan jihar Katsina ta sanar da cafke wani da take zargi da fashi da makami mai shekaru 35. Hukumar ta cafke Usman dan unguwar Kwari, yankin badawa na jihar Kano.

An cafke Usman ne a titin IBB a garin Katsina, babban birnin jihar.

Kamar yadda mai magana da yawun 'yan sandan jihaf, Gambo Isah ya sanar, yace an kama Usman ne da fara motar bas kirar Toyota da aka sace a G9 mobile a titin Audu Bako da ke Kano tare da shi.

Takardar tace, "A yau ranar 10 ga watan Nuwamba, 2019 da misalin karfe 6:30, hukumar 'yan sandan ta yi nasarar cafke wani Ibrahim Usman mai shekaru 35 na Unguwar Kwari, yankin Badawa da ke jihar Kano tare da mota kirar Toyota Coaster. Motar mai mazaunin mutane 35 na da lambar rijista AGL 869 R,

"Motar an saceta ne a ofishin G9 mobile dake titin Audu Bako da ke Kano. Ana cigaba da bincike."

DUBA WANNAN: Wasu abubuwa 5 da jama'a basu sani ba a kan Mamman Daura

A wani cigaba kuma, hukumar 'yan sandan jihar ta cafke babban dilan wiwi din nan mai suna Shamsu Rabiu mai shekaru 23 a duniya. Ta samu busasshen ganye mai yawa a wajensa wanda ake zargi wiwi ce.

Kamar yadda mai magana da yawun hukumar ya sanar da manema labarai, yace Shamsu Rabiu dan asalin kauyen Mutum Daya ne da ke kararmar hukumar Kusada ta jihar Katsina. An kamasa ne da jakkuna biyu kunshe da busasshen ganye da ake zargin wiwi ce a lokacin da aka cafkesa.

Ya ce, "An cafke wanda ake zargin ne yayin da yake kokarin kai hajarsa wani wuri. Tuni ya amsa laifinsa kuma yana taimakawa jami'an tsaro wajen bincike. An bankado wasu gungun barayi a jihar Katsina yayin bikin maulidin Sheikh Ahmad Tijjani da aka yi a filin wasa na Muhammad Dikko."

Barayin sun kware a satar kudi, wayoyi da sauran abubuwa masu amfani. Sun kuma amsa laifukan da suka aikata a fadin jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel