Masarautar Bakundi ta karrama jigon jam'iyyar PDP da sarauta

Masarautar Bakundi ta karrama jigon jam'iyyar PDP da sarauta

An nada shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na jihar Taraba, Mista Victor Bala Kona a matsayin Garkuwan Bakundi.

Sarkin Bakundi, Alhaji Muhammad Misa Gidado ne ya nadawa Mista Bala Kona sarautar Garkuwan Bakundi a fadarsa da ke hedkwatan masarautar Bakundi kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A cikin jawabin da ya yi bayan nadin sarautar, sabon Garkuwan Mista Victor Kona ya mika godiyarsa ga Sarkin Bakundi, Alhaji Muhammed Misa Gidado nada shi daya daga cikin mukammai masu daraja a masarautar.

Ya yi mubaya'a ga sarkin Bakundi da dukkan al'ummar masauratar.

DUBA WANNAN: Wasu abubuwa 5 da jama'a basu sani ba a kan Mamman Daura

Ya tabbatarwa Sarkin na Bakundi cewa zai yi aiki tare da fadar sarkin domin kawo zaman lafiya da cigaba a masarautar.

Gwamnan jihar Taraba Darius Ishaku wanda ya samu wakilcin Lamdo Gashaka, Alhaji Zubairu Hamangabdo a wurin bikin nadin sarautar ya ce masaratun gargajiya suna taka muhimmiyar rawa wurin kawo zaman lafiya da cigaba a jihar.

Ya tabbatarwa masu rike da sarautun gargajiya cewa gwamnatinsa za ta cigaba da ba su goyon baya.

Gwamna Darius ya taya sabon Garkuwar murna inda ya ce an nada sarautar ne saboda irin gudunmawar da ya ke bawa masarautar ta Bakundi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel