Amarya ta kone dan kishiyarta saboda tayi mafarki yana saduwa da ita

Amarya ta kone dan kishiyarta saboda tayi mafarki yana saduwa da ita

- Wata mata ta bayyana yadda ta saka aka kone dan kishiyarta bayan ta ganshi yana saduwa da ita a mafarki

-Ta ce ta ga dan mijin nata yana saduwa da ita a mafarki, don haka ne ta kaishi wajen mai maganin gargajiya inda yayi amfani da garwashin wuta ya kona hannaye da fuskar yaron

- Hukumar 'yan sanda sun tabbatar da aukuwar wannan lamarin tare da tabbatar da za a gurfanar da wadanda ake zargin

Wata mata mai shekaru 35 a duniya wacce ke dauke da juna biyu ta kai dan mijinta wajen mai maganin gargajiya inda ya kona hannayensa da fuskarsa.

A yayin da yaron mai su a Friday dan shekaru 13 ke bayyana yanda lamarin ya faru ya ce, Jummai ta zargesa da maita inda daga baya ta mikasa ga mai maganin gargajiya.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, Friday na karkashin kulawar Jummai ne a Wulko da ke karamar hukumar Nasarawa-Eggon da ke jihar Nasarawa. Ta sanar da mai maganin gargajiyar yadda dan mijin nata ya sadu da ita a mafarki.

Friday yace, "Matar mahaifina tace tana yawan ganina a mafarki ina saduwa da ita amma na sanar da ita hakan ba gaskiya bane."

Wanda abin ya faru dashi yace, tashi kawai yayi da safe yaga hannayensa sun kumbura.

KU KARANTA: Babbar magana: Mahaifina da kanshi yake duba budurcina ya tabbatar da babu matsala - Jaruma Halima Abubakar

"Sai ta fara min barazanar cewa ba zata zauna dani a gida daya ba, daga nan ne tace zata kaini wajen mai maganin gargajiya."

Kamar yadda Friday ya sanar, "mai maganin gargajiyar Bafulatani ne, ya dau dutse ya jefe ni dashi, daga nan ya gogamin dutse kuma ya kulle hannayena da igiya."

"Ya debo garwashi tare da watsamin, ya umarce ni da in fadi gaskiyar lamarin don ni maye ne kuma dan kungiyar asiri, na sanar dashi bansan komai ba akan abinda suke zargina."

"Ya kara debo yaji ya watsa a wuta inda hayakin ya dinga dukan fuskata yayin da hannayena ke konewa. Daga nan ne na fara addu'a. Bayan nan ne yazo ya kwance ni."

Yayin tabbatar da aukuwar lamarin a ofishin 'yan sandan Wulko, Danjuma Bujujin, jami'in da ke kula da ofishin, yace 'yan sanda na kokarin ganin an gurfanar da wadanda suka aikata laifin.

An gano cewa, an tura fayel dinsu zuwa hedkwatar 'yan sandan yankin Nasarawa-Eggon don zurfafa bincike.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel