Allah yayi wa Ore Falomo, likitan MKO Abiola rasuwa

Allah yayi wa Ore Falomo, likitan MKO Abiola rasuwa

- Ubangiji yayi wa likitan MKO Abiola, Ore Falomo rasuwa

- An ruwaito cewa, ya rasu ne a asibitinsa na Maryland dake jihar Legas a yau Asabar, 9 ga watan Nuwamba

- Falomo shakikin aboki ne ga marigayi Abiola, wanda ya lashe zaben 12 ga watan Yuni, 1993

Majiya daga asibitinsa na Maryland da ke Legas ta tabbatar da rasuwar likitan marigayi MKO Abiola da wurin karfe 2 na daren yau bayan gajeriyar rashin lafiya kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Sanannen likitan, Falomo, ya kasance likitan sanannun 'yan Najeriya da suka hada da manyan shuwagabannin soji, sarakuna, 'yan kasuwa da sauran masu fada a ji.

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa hukumar kwastam ta hana kai man fetur garuruwa kusa da iyakoki

Tabbas ya fuskanci wata irin azaba daga hukumar soji wacce ta hana shi ganin wanda ya lashe zaben 12 ga watan Yuni na shekarar 1993 bayan da aka rufeshi.

Marigayi Chief Gani Fawehinmi ya dau fushi da babban likitan bayan da aka barshi ya ga Abiola amma babu kayan aiki. Babban aboki ne ga Abiola wanda iyalansa ke matukar girmamawa.

Hakazalika, jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Mohammed Babangida, daya daga cikin 'ya'yan tsohon shugaban kasar mulkin soja, Ibrahim Babangida, ya bayyana cewa, sun sha mamaki a lokacin da mahaifinsu ya sanar da ya soke zaben ranar 12 ga watan Yuni, 1993 din.

Mohammed yace, mahaifinshi ya maida musu da martanin cewa: "Kun yi yarinta da ku gane sirrin shugabanci... Akwai yuwuwar wannan abun ya dameni har karshen rayuwata."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel