Bidiyo: Jama'a sun muzanta wani dan sanda da ya fadi a titi bayan ya yi tatul da giya

Bidiyo: Jama'a sun muzanta wani dan sanda da ya fadi a titi bayan ya yi tatul da giya

Wani bidiyo da ke nuna jami’in dan sandan Najeriya cikin halin maye kwance a kasa ya billo a kafofin sadarwa na itanet, inda mutane da ke wucewa suka dunga yi masa ba’a tare da muzanta shi.

A cikin bidiyon wanda ya kai kimanin sakwan 30, an gano dan sandan mai matsakaicin shekaru sanye cikin inifam dinsa, cikin halin maye inda yake rike da wani abu da aka nade wanda ba a san ko menene ba.

An kuma jiyo muryoyin mutanen da ke kewaye dashi wadanda sune ke daukarsa bidiyo suna masa wasu tambayoyi cikin izgili yayinda shi kuma yake amsa masu da gwarancin turanci.

“Ni dan sandan Najeriya ne,” inji jami’in.

Ina bindigarka?” Daya daga cikin masu wucewar ya tambaya. “Bani da bindiga,” ya mayar masa da martani.

“Ba su baka ba ko kuma ka siyar?” Ya tambaya cikin dariya. “A’a, ban da bindiga fa,” inji dan sandan.

“Me yasa ba su baka bindiga ba?” Ya cigaba da tambaya. “Saboda zan kashe mutane,” inji dan sandan.

Amsar da ya bayar ya sa aka fashe da dariya a tsakanin masu masa tambayoyin. “wannan dan sandan Najeriya na fa,” suka hada baki.

Ga bidiyon a kasa:

A wani labari na daban, mun ji cewa a yau ne wasu jami’an tsaro dake gadin mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo suka sauke fushinsu a kan wani dan jarida mai daukan hoto dake aiki da gidan jaridar Vanguard, inda suka lakada masa dan banzan duka.

Jaridar The Cable ta ruwaito lamarin ya faru ne a cikin fadar gwamnatin Najeriya, Aso Rock Villa, yayin da Osinbajo ya halarci taron hukumar kula da yan Najeriya mazauna kasashen waje daya gudana a babban dakin taro na Villa.

A wannan lokaci ne dan jaridar mai suna Adeshida Abayomi ya tsaya yana daukan mataimakin shugaban hotuna, kwatsam sai ya ga jami’an hukumar tsaro na DSS sun far masa, suka shiga dukansa, suna jan shi a kasa, tare da farfasa masa na’urar daukan hotonsa.

Duk wannan lamari ya faru ne a gaban mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, amma ko uffan bai ce ba, babu abin da ya yi domin ya hanasu, sai dai babban dogarinsa ne ya sa baki suka kyale shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel